Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 2:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Amma idan kun tuna mini mafarkin, duk da fassararsa, to, zan ba ku lada, da kyautai, da girma mai yawa. Don haka sai ku faɗa mini mafarkin, duk da fassararsa.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Amma in har kuka faɗa mini mafarkina kuka kuma bayyana fassararsa, za ku sami lada mai girma. Saboda haka ku faɗa mini mafarkin da kuma fassararsa.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 2:6
8 Iomraidhean Croise  

Sai sarki ya ba Daniyel girma mai yawa, da manya manyan kyautai masu yawa. Ya kuma naɗa shi mai mulki bisa dukan lardin Babila. Ya shugabantar da shi bisa dukan masu hikima waɗanda suke Babila.


Sai Belshazzar ya ba da umarni, aka sa wa Daniyel rigar shunayya, aka sa sarƙar zinariya a wuyansa, aka kuma yi shela, cewa yanzu shi ne na uku cikin masu mulkin ƙasar.


Sai sarki ya yi kira da babbar murya, cewa a kawo masu dabo, da bokaye, da masu duba. Sai sarki ya ce wa masu hikima na Babila, “Dukan wanda ya karanta wannan rubutu, ya faɗa mini ma'anarsa, to, za a sa masa rigar shunayya, a kuma sa masa sarƙar zinariya a wuyansa, zai zama shi ne na uku a cikin masu mulkin ƙasar.”


gama zan ɗaukaka ka ƙwarai, kome kuwa ka faɗa mini in yi, zan yi, ka zo ka la'anta mini wannan jama'a.’ ”


Sai Balak ya ce wa Bal'amu, “Ashe, ban aika a kirawo ka ba? Me ya sa ba ka zo wurina ba, sai yanzu? Ko ban isa in ɗaukaka ka ba ne?”


Dattawan Mowab da na Madayana suka ɗauki kafin alkalami suka tafi wurin Bal'amu suka faɗa masa saƙon Balak.


Yanzu sai ka tafi abinka. Hakika, na ce zan ɗaukaka ka, amma ga shi, Ubangiji ya hana maka ɗaukakar.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan