Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 2:49 - Littafi Mai Tsarki

49 Daniyel kuwa ya roƙi sarki ya naɗa Shadrak, da Meshak, da Abed-nego su zama masu kula da harkokin lardin Babila, amma Daniyel yana fādar sarki.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

49 Bugu da ƙari, bisa ga bukatar Daniyel sai sarki yă naɗa Shadrak da Meshak da Abednego su zama masu kula da harkokin lardin Babilon, amma Daniyel kuma ya tsaya a fadar sarki.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 2:49
12 Iomraidhean Croise  

Sa'ad da aka tara budurwai a karo na biyu, Mordekai yana zaune a ƙofar sarki.


A kwanakin nan sa'ad da Mordekai yake zaune a ƙofar sarki, sai babani biyu na sarki, wato Bigtana da Teresh waɗanda suke tsaron ƙofar, suka yi fushi, har suka nema su kashe sarki Ahasurus.


Dukan barorin sarki waɗanda suke a bakin ƙofar sarki suka rusuna suka yi wa Haman mubaya'a, gama sarki ya umarta a yi masa haka. Amma Mordekai bai rusuna ya yi masa mubaya'a ba.


Sa'ad da mutanen kirki suke sarauta, kowa da kowa yakan yi biki, amma sa'ad da mugaye suka kama mulki mutane sukan riƙa ɓuya.


Sa'an nan da aka ci Urushalima, sai dukan sarakunan Sarkin Babila suka shiga, suka zauna a Ƙofar Tsakiya. Sarakuna, su ne Nergal-sharezer, da Samgar-nebo, da Sarsekim, wato Rabsaris, da Nergal-sharezer, wato Rabmag, da dukan sauran shugabannin Sarkin Babila.


Waɗannan samari huɗu kuwa, Allah ya ba su ilimi, da sanin littattafai, da hikima. Ya kuma yi wa Daniyel baiwar ganewar wahayi da mafarkai.


Sai sarkin fāda ya laƙaba musu sababbin sunaye. Ya kira Daniyel, Belteshazzar, ya kira Hananiya, Shadrak, ya kira Mishayel, Meshak, sa'an nan ya kira Azariya, Abed-nego.


Sai Daniyel ya tafi gidansa, ya sanar wa abokansa, wato su Hananiya, da Mishayel, da Azariya da al'amarin.


Sarki Nebukadnezzar ya yi gunki na zinariya wanda tsayinsa kamu sittin ne, fāɗinsa kuma kamu shida. Ya kafa shi a filin Dura wanda yake a lardin Babila.


Sai ya naɗa Daniyel da waɗansu mutum biyu su zama shugabannin muƙaddasan nan. Su muƙaddasan kuwa za su riƙa ba shugabannin labarin aikinsu, don kada sarki ya yi hasarar kome.


Ku ƙi mugunta, ku ƙaunaci nagarta, Ku yi adalci cikin majalisar alƙalanku! Watakila Ubangiji Allah Mai Runduna Zai yi wa sauran da suka ragu na wannan al'umma alheri.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan