Daniyel 2:48 - Littafi Mai Tsarki48 Sai sarki ya ba Daniyel girma mai yawa, da manya manyan kyautai masu yawa. Ya kuma naɗa shi mai mulki bisa dukan lardin Babila. Ya shugabantar da shi bisa dukan masu hikima waɗanda suke Babila. Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 202048 Sai sarki ya ɗora Daniyel a babban matsayi ya kuma sanya shi mai mulki a kan dukan yankin ƙasar Babilon; ya kuma ɗora shi yă zama mai kula da duk masu hikima. Faic an caibideil |
Sai sarki ya yi kira da babbar murya, cewa a kawo masu dabo, da bokaye, da masu duba. Sai sarki ya ce wa masu hikima na Babila, “Dukan wanda ya karanta wannan rubutu, ya faɗa mini ma'anarsa, to, za a sa masa rigar shunayya, a kuma sa masa sarƙar zinariya a wuyansa, zai zama shi ne na uku a cikin masu mulkin ƙasar.”