Daniyel 2:47 - Littafi Mai Tsarki47 Ya kuma ce wa Daniyel, “Hakika, Allahnka, Allahn alloli ne da Ubangijin sarakuna, mai bayyana asirai, gama ka iya bayyana wannan asiri.” Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 202047 Sarki ya kuma ce wa Daniyel, “Tabbatacce Allahnka shi ne Allahn alloli da kuma Sarkin sarakuna da mai bayyana asirai, gama ka iya bayyana wannan asiri.” Faic an caibideil |
Yanzu, idan kuna so, sa'ad da kuka ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai ku fāɗi ƙasa, ku yi sujada ga gunkin zinariya da na kafa. Idan kun yi haka, da kyau. Amma idan ba ku yi sujadar ba, nan take za a jefa ku a tanderun gagarumar wuta, in ga ko wane ne allahn nan da zai kuɓutar da ku daga hannuna?”
Nebukadnezzar ya ce, “Yabo ya tabbata ga Allah na Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, wanda ya aiko da mala'ikansa, ya ceci bayinsa masu dogara gare shi, waɗanda kuma ba su yarda su bi umarnin sarki ba, amma suka gwammace a ƙone su maimakon su bauta wa gunki, ko su yi masa sujada, sai dai ga Allahnsu kaɗai.