Daniyel 2:45 - Littafi Mai Tsarki45 Kamar yadda ka ga an gutsuro dutse ba da hannun ɗan adam ba, ya kuwa ragargaje baƙin ƙarfen, da tagullar, da yumɓun, da azurfar, da zinariyar, Allah Maɗaukaki ya sanar wa sarki abin da zai faru nan gaba. Mafarkin tabbatacce ne, fassarar kuma gaskiya ce.” Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 202045 Wannan shi ne ma’anar wannan wahayin da ka gani na dutsen da aka yanko daga jikin tsaunin, amma ba da hannun ɗan adam ba, dutsen da ya ragargaza ƙarfen, da tagullar, da yumɓun da azurfar da kuma zinariyar. “Allah mai girma ya nuna wa sarki abin da zai faru nan gaba. Mafarkin gaskiya ne, fassararsa kuma abin dogara ne.” Faic an caibideil |
“Ya Allah, Allahnmu, da girma kake! Kai mai banrazana ne, cike da iko! Da aminci ka cika alkawaranka da ka alkawarta. Daga lokacin da Sarkin Assuriya ya danne mu, Har yanzu ma, wace wahala ce ba mu sha ba! Sarakunanmu, da shugabanninmu, da firistocinmu, Da annabawanmu, da kakanninmu, Da dukan sauran jama'arka sun sha wahala. Ka san irin wahalar da muka sha.