Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 2:42 - Littafi Mai Tsarki

42 Kamar yadda yatsotsin ƙafafun rabi baƙin ƙarfe, rabi kuma yumɓu ne, haka nan mulkin zai kasance, rabi da ƙarfi, rabi kuma da gautsi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

42 Kamar yadda yatsotsin rabi na ƙarfe rabi kuma na yumɓu ne, haka wannan mulki zai zama rabi mai ƙarfi rabi kuma marar ƙarfi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 2:42
4 Iomraidhean Croise  

Ka kuma ga an yi ƙafafun da yatsotsin da baƙin ƙarfe gauraye da yumɓu, wato mulkin zai rabu, amma zai kasance da ƙarfi kamar na baƙin karfen da yake gauraye da yumɓu.


Kamar yadda ka ga baƙin ƙarfen ya gauraya da yumɓun, haka nan mulkokin za su gauraye da juna ta wurin aurayya, amma ba za su haɗu da juna ba, kamar yadda baƙin ƙarfe da yumɓu ba su haɗuwa.


Ƙahonin nan goma kuwa, sarakuna goma ne waɗanda za su taso daga cikin mulkin. Sa'an nan wani sarki zai taso a bayansu wanda zai bambanta da sauran da suka fara tasowa, zai kā da sarakuna uku.


Na kuma ga wata dabba tana fitowa daga cikin teku, mai ƙaho goma, da kawuna bakwai, da kambi goma a kan ƙahoninta, da kuma wani suna na saɓo a kawunanta.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan