Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 2:41 - Littafi Mai Tsarki

41 Ka kuma ga an yi ƙafafun da yatsotsin da baƙin ƙarfe gauraye da yumɓu, wato mulkin zai rabu, amma zai kasance da ƙarfi kamar na baƙin karfen da yake gauraye da yumɓu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

41 Ka kuma ga an yi ƙafafun da yatsotsin da baƙin ƙarfe gauraye da yumɓu, wato, mulkin zai rabu, amma zai kasance da ƙarfi kamar na baƙin ƙarfe da yake gauraye da yumɓu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 2:41
8 Iomraidhean Croise  

Za a kuma yi mulki na huɗu, mai ƙarfi kamar baƙin ƙarfe. Da yake baƙin ƙarfe yakan kakkarya, ya ragargaje abubuwa, haka nan wannan mulki zai ragargaje sauran mulkoki.


Kamar yadda yatsotsin ƙafafun rabi baƙin ƙarfe, rabi kuma yumɓu ne, haka nan mulkin zai kasance, rabi da ƙarfi, rabi kuma da gautsi.


Ƙahonin nan goma kuwa, sarakuna goma ne waɗanda za su taso daga cikin mulkin. Sa'an nan wani sarki zai taso a bayansu wanda zai bambanta da sauran da suka fara tasowa, zai kā da sarakuna uku.


“Bayan wannan kuma a wahayi na dare na ga dabba ta huɗu mai ƙarfi ƙwarai, mai bantsoro da banrazana. Tana da haƙoran ƙarfe, zaga-zaga. Ta cinye, ta ragargaza, sa'an nan ta tattake sauran da ƙafafunta. Dabam take da sauran dabbobin da suka riga ta. Tana kuma da ƙaho goma.


Sai kuma aka ga wata alama a sama, ga wani ƙaton jan maciji mai kawuna bakwai, da ƙahoni goma, da kambi bakwai a kawunansa.


Na kuma ga wata dabba tana fitowa daga cikin teku, mai ƙaho goma, da kawuna bakwai, da kambi goma a kan ƙahoninta, da kuma wani suna na saɓo a kawunanta.


Ƙahonin nan goma kuwa da ka gani, sarakuna goma ne, waɗanda ba a naɗa ba tukuna, amma sa'a ɗaya tak, za a ba su ikon yin mulki tare da dabbar.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan