Daniyel 2:4 - Littafi Mai Tsarki4 Sai Kaldiyawa suka yi magana da sarki da Aramiyanci, suka ce, “Ran sarki ya daɗe! Ka faɗa wa barorinka mafarkin, za mu kuwa yi maka fassararsa.” Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 20204 Sai masanan taurarin suka amsa wa sarki da Arameyanci “Ran sarki yă daɗe! Ka faɗa wa bayinka mafarkin, mu kuma sai mu fassara.” Faic an caibideil |
Daniyel kuwa wanda aka laƙaba wa suna Belteshazzar, ya tsaya zugum da ɗan daɗewa, tunaninsa ya ba shi tsoro. Sarki ya ce, “Belteshazzar, kada ka bar mafarkin ko ma'anarsa ya ba ka tsoro.” Sai Belteshazzar ya amsa, ya ce, “Ya shugabana, Allah ya sa mafarkin nan, da ma'anarsa, su zama a kan maƙiyanka.