Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 2:38 - Littafi Mai Tsarki

38 A hannunka kuma ya ba da dukan wurare inda 'yan adam, da dabbobi, da tsuntsaye suke zama. Ya sa ka ka mallake su duka. Kai ne kan zinariyan nan na mutum-mutumin.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

38 a cikin hannunka ya sanya ɗan adam, da namun jeji da tsuntsayen sama. A duk inda suke zaune, ya maishe ka ka yi mulki a bisansu kai ne kan zinariyan nan na siffar.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 2:38
10 Iomraidhean Croise  

Ubangiji ya yi magana da Irmiya sa'ad da Nebukadnezzar, Sarkin Babila, da dukan sojojinsa, da dukan sojojin mulkokin al'umman da suke a ƙarƙashinsa, da dukan mutane suke yaƙi da Urushalima da dukan biranenta.


Ubangiji kuwa ya ba Nebukadnezzar nasara a kan Yehoyakim, Sarkin Yahuza, sai ya kwashe waɗansu kayayyakin Haikalin Allah, ya kawo su ƙasar Shinar a gidan gunkinsu, ya ajiye kayayyakin a baitulmalin gunkinsa.


An yi kan mutum-mutumin da zinariya tsantsa. Ƙirji da damutsa, an yi su da azurfa, cikinsa da cinyoyinsa, an yi su da tagulla.


A bayanka kuma za a yi wani mulki wanda bai kai kamar naka ba. Za a yi wani mulki kuma na uku mai darajar tagulla, wanda zai mallaki dukan duniya.


“Mafarkin da ni sarki Nebukadnezzar na yi ke nan. Kai Belteshazzar kuma, sai ka faɗa mini ma'anarsa, domin dukan masu hikima na cikin mulkina ba su iya faɗar mini ma'anar, amma kai ka iya, gama ruhun alloli tsarkaka yana cikinka.”


“Ya sarki, Allah Maɗaukaki ya ba Nebukadnezzar ubanka sarauta, da girma, da daraja, da martaba.


Kamannin dabba ta fari irin ta zaki ce, amma tana da fikafikan gaggafa. Ina kallo, sai aka fige fikafikanta, aka ɗaga ta sama, aka sa ta tsaya a kan ƙafafu biyu kamar mutum, aka ba ta tunani irin na mutum.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan