Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 2:35 - Littafi Mai Tsarki

35 Sa'an nan baƙin ƙarfen, da yumɓun, da tagullar, da azurfar, da zinariyar suka ragargaje gaba ɗaya, duka suka zama kamar ƙaiƙayi na masussuka da kaka. Iska kuwa ta kwashe su ta tafi da su, har ba a iya ganin ko alamarsu. Amma wannan dutse da ya buge mutum-mutumin ya girke, ya zama babban dutse ya cika duniya duka.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

35 Sai ƙarfen da yambun da tagulla da azurfan da kuma zinariyan suka ragargaje a lokaci ɗaya ya zama kamar ƙaiƙayi a masussuka a lokacin kaka. Sai iska ta kwashe su ta tafi, har ba a iya ganin ko alamarsu. Amma dutsen da ya fāɗo a siffar ya girke ya zama tsauni ya kuma cika dukan duniya.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 2:35
28 Iomraidhean Croise  

Sa'an nan iska ta bi ta kansa, yakan ɓace, Ba mai ƙara ganinsa.


Dukan al'ummai za su tuna da Ubangiji, Za su zo gare shi daga ko'ina a duniya, Dukan kabilai za su yi masa sujada.


A ɗan ƙanƙanen lokaci mugaye za su shuɗe, Za ka neme su, amma ba za a same su ba,


Amma bayan ƙanƙanen lokaci, Da na zaga, ban gan shi ba, Na neme shi, amma ban same shi ba.


Ya hana yaƙoƙi ko'ina a duniya, Yana karya bakkuna, yana lalatar da māsu, Yana ƙone karusai da wuta.


Duk wanda yake a duniya, yana yi maka sujada, Yana raira maka waƙar yabbai, Yana raira yabbai ga sunanka.”


Dukan sauran al'umma da ka halitta Za su zo su rusuna har ƙasa a gabanka. Za su yabi girmanka,


A kan Sihiyona, dutse tsattsarka, Ba wani macuci ko mugu. Ƙasar za ta cika da sanin Ubangiji Kamar yadda tekuna suke cike da ruwa.


Ku tattaru a tsorace ya ku sauran al'umma! Ku saurara, ya ku manisantan wurare na duniya. Ku yi shirin faɗa, amma ku ji tsoro! Hakika ku yi shiri, amma ku ji tsoro!


A kwanakin waɗannan sarakuna, Allah na Sama zai kafa wani mulki wanda ba zai taɓa rushewa ba har abada, ba kuma za a gādar da shi ga waɗansu mutane ba. Wannan mulki zai ragargaje dukan waɗannan mulkoki, ya kawo ƙarshensu. Wannan mulki zai dawwama har abada.


Don haka za su zama kamar ƙāsashin da akan yi da safe, Ko kuwa kamar raɓa mai kakkaɓewa da wuri. Za su zama kamar ƙaiƙayi wanda ake shiƙarsa cikin iska a masussuka, Ko kuwa kamar hayaƙin da yake fita ta bututu.


“Ya Sihiyona, ki tashi, ki tattaka! Gama zan mai da ƙahonki ƙarfe, kofatanki kuwa tagulla, Za ki ragargaje al'ummai da yawa.” Za ki ba Ubangijin dukan duniya dukiyarsu da suka tara ta hanyar zamba, Wadatarsu kuma ga Ubangijin dukan duniya.


A ran nan zan sa Urushalima ta zama dutse mai nauyi ga dukan al'ummai. Duk wanda ya ɗaga ta zai ji wa kansa mugun rauni. Dukan al'umman duniya za su taru su kewaye ta.


Domin kuwa lalle ne ya yi mulki, har ya take dukkan maƙiyansa.


Sa'an nan mala'ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji waɗansu muryoyi masu ƙara a Sama, suna cewa, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa, shi kuma zai yi mulki har abada abadin.”


amma aka cinye su, har suka rasa wuri a sama sam.


Sa'an nan na ga wani babban kursiyi fari, da wanda yake a zaune a kai, sai sama da ƙasa suka guje wa Zatinsa, suka ɓace.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan