Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 2:34 - Littafi Mai Tsarki

34 Sa'ad da kake cikin dubawa, sai aka gutsuro wani dutse ba da hannun mutum ba, aka bugi ƙafafunsa na baƙin ƙarfe gauraye da yumɓu, aka ragargaza shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

34 A lokacin da kake dubawa, sai aka yanko wani dutse, amma ba da hannun mutum ba. Ya fāɗa a kan ƙafafun siffar na ƙarfen da aka haɗa da yumɓu aka kuma ragargaje su.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 2:34
25 Iomraidhean Croise  

Dutsen da magina suka ƙi, wai ba shi da amfani, Sai ya zama shi ya fi duka amfani.


Yanzu fa ga abin da Ubangiji ya ce, “Zan kafa ƙaƙƙarfan harsashin gini a Sihiyona. A kansa zan sa ƙaƙƙarfan dutsen kusurwa. A kansa an rubuta wannan magana, ‘Amincin da yake kafaffe mai haƙuri ne kuma.’


Amma al'umman da ba su bauta miki ba, Za a hallakar da su.


Ku tattaru a tsorace ya ku sauran al'umma! Ku saurara, ya ku manisantan wurare na duniya. Ku yi shirin faɗa, amma ku ji tsoro! Hakika ku yi shiri, amma ku ji tsoro!


Amma za a karya ku, ku kwanta tare da marasa imani, tare da waɗanda aka kashe da takobi.


Ya sāke auna kamu dubu kuma, sai ruwan ya zama kogi har ban iya in haye ba, gama ruwan ya hau, ya zama da zurfin da ya isa ninƙaya. Ya zama kogin da ba za a iya hayewa ba.


Da baƙin ƙarfe aka yi sharaɓansa, an yi ƙafafunsa da baƙin ƙarfe gauraye da yumɓu.


Sa'an nan za a ba da sarauta da girman dukan mulkokin duniya ga tsarkaka na Maɗaukaki. Mulkinsa madawwamin mulki ne. Dukan sarakunan duniya za su bauta masa, su kuma yi masa biyayya.’


Ta wurin mugun wayonsa zai sa cin hanci ya haɓaka. Zai ɗaukaka kansa a ransa. Zai hallaka mutane da yawa, ba zato ba tsammani, har ma zai tasar wa Sarkin sarakuna, amma za a hallaka shi ba ta hannun mutum ba.


A ran nan zan sa Urushalima ta zama dutse mai nauyi ga dukan al'ummai. Duk wanda ya ɗaga ta zai ji wa kansa mugun rauni. Dukan al'umman duniya za su taru su kewaye ta.


Sa'an nan ya ce, “Wannan ita ce maganar Ubangiji zuwa ga Zarubabel cewa, ‘Ba da ƙarfi, ko iko ba, amma da Ruhuna,’ in ji Ubangiji Mai Runduna.


Ina dai gaya maka, kai ne Bitrus, a kan dutsen nan ne zan gina ikilisiyata, wadda ikon Hades ba zai rinjaye ta ba.


wato, waɗanda aka haifa ba daga jini ba, ba daga nufin jiki ko nufin mutum ba, amma daga wurin Allah.


Wannan shi ne dutsen nan da ku magina kuka raina, shi ne kuwa ya zama mafificin dutsen gini.


Gama mun sani in an rushe jikinmu na wannan duniya, Allah ya tanadar mana jiki a Sama, wato, wanda shi kansa ya yi, wanda zai dawwama.


Domin Almasihu bai shiga wani wuri tsattsarka da mutum ya yi ba, wanda yake sura ne kawai na gaskataccen, a'a Sama kanta ya shiga, domin yă bayyana a gaban zatin Allah a yanzu saboda mu.


A gare ku, ku da kuka ba da gaskiya kuwa, shi ɗaukakakke ne. Amma ga waɗanda suka ƙi gaskatawa, to, “Dutsen da magina suka ƙi, Shi ne ya zama mafificin dutsen gini,”


Sa'an nan mala'ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji waɗansu muryoyi masu ƙara a Sama, suna cewa, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa, shi kuma zai yi mulki har abada abadin.”


Za su yi yaƙi da Ɗan Ragon, Ɗan Ragon kuwa zai cinye su, shi da waɗanda suke tare da shi, kirayayyu, zaɓaɓɓu, amintattu, domin shi ne Ubangijin iyayengiji.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan