Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 2:32 - Littafi Mai Tsarki

32 An yi kan mutum-mutumin da zinariya tsantsa. Ƙirji da damutsa, an yi su da azurfa, cikinsa da cinyoyinsa, an yi su da tagulla.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

32 An yi kan wannan siffa da zinariya zalla, ƙirjinta da kuma hannuwanta an yi su da azurfa, cikinta da kuma cinyarta da tagulla ne.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 2:32
11 Iomraidhean Croise  

Sa'ad da ya aikata wannan za su yi wa Sarkin Babila ba'a. Za su ce, “Mugun sarkin ya fāɗi, ba zai ƙara zaluntar kowa ba!


Babila ta zama ƙoƙon zinariya a hannun Ubangiji, Ta sa dukan duniya ta yi maye. Ƙasashen duniya sun sha ruwan inabinta, suka haukace.


Da baƙin ƙarfe aka yi sharaɓansa, an yi ƙafafunsa da baƙin ƙarfe gauraye da yumɓu.


kai ne wannan itace, ya sarki. Ka yi girma, ka ƙasaita. Girmanka ya kai har sama, mulkinka kuma ya kai ko'ina a duniya.


sai ya ce, “Ashe, wannan ba ita ce Babila babba wadda ni da kaina na gina, da ƙarfin ikona don ta zama fādar sarauta, don darajar ɗaukakata?”


Ma'anar PERES ita ce an raba mulkinka, an ba mutanen Mediya da na Farisa.”


Matar kuwa tana saye da tufafi masu ruwan jar garura, da kuma ja wur, ta ci ado da kayan zinariya, da duwatsun alfarma, da lu'ulu'u, tana a riƙe da ƙoƙon zinariya a hannunta, cike da abubuwan ƙyama, da ƙazantar fasikancinta.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan