Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 2:27 - Littafi Mai Tsarki

27 Daniyel ya amsa wa sarki, ya ce, “Ba masu hikima, ko masu dabo, ko masu sihiri, ko masu duba, da za su iya su warware wa sarki wannan matsala da ta dame shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

27 Daniyel ya amsa, “Babu wani mai hikima, ko mai sihiri, ko mai dabo ko mai duban da zai iya warware wa sarki wannan matsala da ta dame shi,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 2:27
12 Iomraidhean Croise  

Suka ce masa, “Mafarkai muka yi, ba kuma wanda zai fassara mana su.” Sai Yusufu ya ce musu, “Ashe, ba a wurin Allah fassarori suke ba? Ku faɗa mini su, ina roƙonku.”


Saboda haka da safe, hankalinsa ya tashi, sai ya aika aka kirawo dukan bokayen Masar da dukan masu hikimar Masar, Fir'auna kuwa ya faɗa musu mafarkansa, amma ba wanda ya iya fassara masa su.


Zan warware shirye-shiryen Masarawa in sa ku karai. Za su roƙi taimako ga gumakansu, za su je kuma su yi shawara da mabiyansu, su kuma nemi shawarar kurwar matattu.


Na sa masu duba su zama wawaye, Na sassāke annabce-annabcen masanan taurari. Na bayyana kuskuren maganar masu hikima, Na kuma nuna masu hikimarsu wauta ce.


Wane ne ba zai ji tsoronka ba, ya Sarkin dukan al'ummai? Ka isa a ji tsoronka, Gama babu kamarka a cikin dukan masu hikima na al'ummai, Da kuma cikin dukan mulkokinsu, Ba wani kamarka.


A cikin dukan abin da ya shafi hikima da ganewa wanda sarki ya nemi shawararsu, sai ya tarar sun fi dukan masu sihiri da bokaye waɗanda suke cikin mulkinsa har sau goma.


Sai sarki ya umarta a kirawo masa masu sihiri, da masu dabo, da bokaye, da Kaldiyawa, su zo su fassara masa mafarkin da ya yi. Sai suka hallara a gaban sarki.


Sai masu sihiri, da masu dabo, da Kaldiyawa, da masu duba suka zo, na faɗa musu mafarkin, amma ba su iya yi mini fassararsa ba.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan