Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 2:23 - Littafi Mai Tsarki

23 A gare ka nake ba da godiya da yabo, ya Allah na kakannina, Gama ka ba ni hikima da iko, Har ka sanar mini da abin da muka roƙe ka, Ka sanar mana da matsalar da ta dami sarki.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 Na gode maka ina yabonka, Allah na kakannina. Kai ka san hikima da iko, ka sanar da ni abin da muka tambaye ka, ka kuma sanar da mu mafarkin sarki.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 2:23
33 Iomraidhean Croise  

Ubangiji ya ce, “Zan ɓoye wa Ibrahim abin da nake shirin aikatawa?


Da ba domin Allah na mahaifina da Ibrahim, da martabar Ishaku na wajena ba, hakika da yanzu ka sallame ni hannu wofi. Allah ya ga wahalata da aikin hannuwana, ya kuwa tsauta maka a daren jiya.”


A lokacin miƙa hadaya ta maraice, sai annabi Iliya ya matso kuwa, ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Ibrahim, da Ishaku, da Isra'ila, bari ya zama sananne a wannan rana, cewa kai ne Allah a Isra'ila, ni kuma bawanka ne, na yi waɗannan abubuwa duka bisa ga maganarka.


Ya Ubangiji Allah, sai ka kasance tare da mu kamar yadda ka kasance tare da kakanninmu, kada ka rabu da mu, ko ka yashe mu.


Dawuda ya yabi Ubangiji a gaban dukan taron, ya ce, “Ya Ubangiji Allah na kakanmu Yakubu, yabo ya tabbata gare ka har abada abadin!


Yanzu ya Allahnmu, muna gode maka muna kuma yabon sunanka mai daraja.


ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na kakanninmu, kai ne Allah na cikin Sama, kai ne kuma kake mulkin dukan al'umman duniya. A gare ka iko da ƙarfi suke, don haka ba wanda ya isa ya jā da kai.


Ka biya masa bukatarsa, Ka amsa roƙonsa.


Ya roƙi rai, ka kuwa ba shi mai tsawo, Da yawan kwanaki.


Ubangiji yakan amince da waɗanda suke biyayya da shi, Yakan koya musu alkawarinsa.


Bari ku miƙa wa Allah hadayarku ta godiya, Ku ba Mai Iko Dukka, dukan hadayun da kuka alkawarta.


Allah kuma ya sāke ce wa Musa, “Faɗa wa Isra'ilawa cewa, ‘Ubangiji Allah na kakanninku, wato na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu ya aiko ni gare ku.’ Wannan shi ne sunana har abada. Da wannan suna za a tuna da ni a dukkan zamanai.


Sarkin yaƙi mai wayo yakan ci birnin da jarumawa suke tsaro, ya rushe garun da suke taƙama da shi.


Mai hikima ƙaƙƙarfa ne, i, mai ilimi yana daɗa ƙarfi.


Nakan shirya abin da zan yi, in kuwa yi shi. Ina da fahimi, ina da ƙarfi.


Abin da hikima take iya yi wa mutum ɗaya ya fi abin da masu mulki goma za su yi wa birni.


Na ce hikima ta fi ƙarfe ƙarfi, ko da yake an raina hikimar matalauci da maganarsa.


Hikima ta fi makaman yaƙi, amma mai zunubi ɗaya yakan yi ɓarna mai yawa.


Rana tana zuwa sa'ad da jama'a za su raira waƙa, su ce, “Ina yabonka ya Ubangiji! A dā ka yi fushi da ni, Amma yanzu kana yi mini ta'aziyya, ba za ka ƙara yin fushi da ni ba.


“Ka kira ni, ni kuwa zan amsa maka, zan kuwa nuna maka manyan al'amura masu girma da banmamaki, waɗanda ba ka sani ba.”


Waɗannan samari huɗu kuwa, Allah ya ba su ilimi, da sanin littattafai, da hikima. Ya kuma yi wa Daniyel baiwar ganewar wahayi da mafarkai.


Ya faɗa musu su nemi jinƙai daga wurin Allah na Sama game da wannan matsala, domin kada Daniyel da abokansa su halaka tare da sauran masu hikima a Babila.


Hakika Ubangiji ba yakan aikata kome ba, Sai da sanin bayinsa annabawa.


A wannan lokaci sai Yesu ya ce, “Na gode maka ya Uba, Ubangijin Sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan al'amura ga masu hikima da masu basira, ka kuma bayyana su ga jahilai.


A wannan lokaci ya yi farin ciki matuƙa ta Ruhu Mai Tsarki, ya ce, “Na gode maka ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan al'amura ga masu hikima da masu basira, ka kuma bayyana su ga jahilai. Hakika na gode maka ya Uba, domin wannan shi ne nufinka na alheri.


Sai suka kawar da dutsen. Yesu kuwa ya ɗaga kai sama ya ce, “Ya Uba, na gode maka da ka saurare ni.


Nan gaba ba sauran in ce da ku bayi, don bawa bai san abin da ubangijinsa yake yi ba. Sai dai in ce da ku aminai, domin na sanar da ku duk abin da na jiyo wurin Ubana.


Wahayin Yesu Almasihu da Allah ya ba shi ya nuna wa bayinsa abin da lalle ne zai auku ba da daɗewa ba, ya kuwa bayyana shi ta wurin aiko da mala'ikansa zuwa gun bawansa Yahaya,


Sai ɗaya daga cikin dattawan nan ya ce mini, “Kada ka yi kuka. Ga shi, Zakin nan na kabilar Yahuza, Tsatson Dawuda, ya ci nasara har yake da iko yă buɗe littafin nan da hatimansa bakwai.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan