Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 2:22 - Littafi Mai Tsarki

22 Yana bayyana zurfafan abubuwa masu wuyar ganewa, Ya san abin da yake cikin duhu. Haske kuma yana zaune tare da shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

22 Yakan bayyana zurfafa da ɓoyayyun abubuwa; ya san abin da yake cikin dare, haske kuwa yana zaune tare da shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 2:22
37 Iomraidhean Croise  

Yusufu ya amsa wa Fir'auna ya ce, “Ba a gare ni ba, Allah zai amsa wa Fir'auna da kyakkyawar amsa.”


Yakan aika da haske a wuraren da suke da duhu kamar mutuwa.


Lahira tsirara take a gaban Allah, Haka kuma Halaka take a gaban Allah.


Ka yi lulluɓi da haske. Ka shimfiɗa sammai kamar alfarwa.


Ubangiji yakan amince da waɗanda suke biyayya da shi, Yakan koya musu alkawarinsa.


Kai ne mafarin dukan rai, Saboda haskenka ne kuma, muke ganin haske.


Mutum mai hikima ne kaɗai ya san ainihin ma'anar yadda abubuwa suke. Hikima takan sa shi fara'a, da sakin fuska.


Ku zo nan ku faɗi abin da zai faru nan gaba, Ku bayyana wa ɗakin shari'a abubuwan da suka riga sun faru, Ku faɗa mana yadda zai zama duka, Domin lokacin da ya faru mu mu sani.


Wane ne a cikinku ya faɗa mana tun da wuri, Ko ya yi annabci, cewa wannan zai faru, Har da za mu ce kun yi daidai? Ba ko ɗayanku da ya ce tak a kan wannan, Ba kuwa wanda ya ji kuna faɗar wani abu!


Abubuwan da na faɗa yanzu sun cika. Yanzu zan faɗa muku sababbin abubuwa, Tun kafin ma su soma faruwa.”


Ni na halicci haske duk da duhu, Ni ne na kawo albarka duk da la'ana. Ni Ubangiji, na yi dukkan waɗannan abu.


“Mutum ya iya ɓoye kansa a wani lungu Inda ba zan iya ganinsa ba?” In ji Ubangiji. “Ashe, ban cika sammai da duniya ba?


“Ka kira ni, ni kuwa zan amsa maka, zan kuwa nuna maka manyan al'amura masu girma da banmamaki, waɗanda ba ka sani ba.”


Abin nan da sarki yake so a yi masa yana da wuya, ba wanda zai iya biya wa sarki wannan bukata, sai dai ko alloli waɗanda ba su zama tare da 'yan adam.”


Sai aka bayyana wa Daniyel asirin ta cikin wahayi da dare. Daga nan Daniyel ya yabi Allah na Sama.


Ya kuma ce wa Daniyel, “Hakika, Allahnka, Allahn alloli ne da Ubangijin sarakuna, mai bayyana asirai, gama ka iya bayyana wannan asiri.”


Ai, a cikin mulkinka akwai wani mutum wanda yake da ruhun alloli tsarkaka. A zamanin ubanka, an iske fahimi, da ganewa, da hikima irin na alloli a cikinsa. Sarki Nebukadnezzar ubanka, ya naɗa shi shugaban masu sihiri, da masu dabo, da bokaye, da masu duba.


Na ji labari, cewa kana da ruhun alloli tsarkaka, da fahimi, da ganewa, da mafificiyar hikima.


Shi ya sa nake musu magana da misalai, don ko sun duba ba sa gani, ko sun saurara ba sa ji, ba sa kuma fahimta.


Akwai hakikanin haske mai shigowa duniya da yake haskaka kowane mutum.


Yesu ya faɗa masa, faɗa ta uku, “Bitrus ɗan Yahaya, kana sona?” Sai Bitrus ya yi baƙin ciki don a faɗar nan ta uku ya ce masa, “Kana sona?” Shi kuwa ya ce masa, “Ya Ubangiji, ai, ka san kome duka, ka kuwa sani ina sonka.” Yesu ya ce masa, “Ka yi kiwon tumakina.


Sai Yesu ya ƙara musu da cewa, “Ni ne Hasken duniya. Wanda yake bi na ba zai yi tafiya a duhu ba, amma zai sami hasken rai,”


Don haka, kada ku yanke wani hukunci tun lokaci bai yi ba, kafin komowar Ubangiji, wanda zai tone al'amuran da suke ɓoye a duhu, ya kuma bayyana nufin zukata. A sa'an nan ne, Allah zai yaɓa wa kowa daidai gwargwado.


wanda a zamanin dā ba a sanar da 'yan adam ba, kamar yadda a yanzu aka bayyana wa manzanninsa tsarkaka da annabawa, ta wurin Ruhu,


Ubangiji ya tumɓuke su da zafin fushinsa, da babbar hasala, daga ƙasarsu, ya watsa su cikin wata ƙasa dabam kamar yadda suke a yau.’


Shi ne kaɗai marar mutuwa, yake kuma zaune a cikin hasken da ba ya kusatuwa. Shi kuwa ba mutumin da ya taɓa ganinsa, ko kuwa zai iya ganinsa. Girma da madawwamin mulki su tabbata a gare shi. Amin, amin.


Ba wata halittar da za ta iya ɓuyar masa, amma kowane abu a fili yake, a shanye sosai a gaban idon wannan da za mu ba da lissafi a gabansa.


Kowace kyakkyawar baiwa, da kowace cikakkiyar kyauta, daga Sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.


Wannan shi ne jawabin da muka ji a gunsa, muke sanar da ku cewa Allah haske ne, ba kuwa duhu gare shi ko kaɗan.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan