Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 2:20 - Littafi Mai Tsarki

20 Ya ce, “Yabo ya tabbata ga sunan Allah har abada abadin, Wanda hikima da iko nasa ne.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

20 Ya ce, “Yabo ya tabbata ga sunan Allah har abada abadin; hikima da iko nasa ne.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 2:20
25 Iomraidhean Croise  

Ga Allah Maɗaukaki yabo ya tabbata, shi wanda ya ba ka maƙiyanka a tafin hannunka!” Abram kuwa ya ba shi ushiri na duka.


“Yabo ya tabbata ga Ubangiji wanda ya hutar da jama'arsa, Isra'ilawa, bisa ga yadda ya alkawarta. Daga cikin abin da ya alkawarta duka na alheri ba ko ɗaya da bai cika ba, kamar yadda ya alkawarta wa bawansa, Musa.


Sa'an nan Dawuda ya ce wa taro duka, “Sai ku yabi Ubangiji Allahnku yanzu.” Taron jama'a kuwa suka yabi Ubangiji Allah na kakanninsu, suka rusuna har ƙasa, suka yi wa Ubangiji sujada, suka kuma girmama sarki.


Sa'ad da ya yi shawara da jama'a, sai ya zaɓi waɗanda za su raira waƙa ga Ubangiji, su yabe shi a natse sa'ad da suke tafe a gaban runduna, su ce, “Ku yi godiya ga Ubangiji, Saboda madawwamiyar ƙaunarsa Tabbatacciya ce har abada.”


Waɗannan Lawiyawa kuma, wato Yeshuwa, da Kadmiyel, da Bani, da Hashabnaiya, da Sherebiya, da Hodiya, da Shebaniya, da Fetahiya su ne suka yi kiran sujada, suka ce, “Ku miƙe tsaye, ku yabi Ubangiji Allahnku, Ku yabe shi har abada abadin. Bari kowa ya yabi maɗaukakin sunanka, ya Ubangijii, Ko da yake ba yabon da ɗan adam zai yi har ya isa.”


Yabo Ya tabbata ga Ubangiji! Ku bayin Ubangiji, Ku yabi sunansa!


Za a yabi sunansa yanzu da har abada!


Amma mu da muke rayayyu, za mu yi masa godiya. A yanzu da har abada. Yabo ya tabbata ga Ubangiji!


Ubangijinmu mai girma ne, Mai Iko Dukka, Saninsa ya fi gaban aunawa.


Bari mu yabi Ubangiji, Allah na Isra'ila. Ku yabe shi yanzu da har abada! Amin! Amin!


Wanda yake yin godiya a sa'ad da yake miƙa hadayarsa, yana girmama ni, Da wanda yake yi mini biyayya kuma, zan nuna masa cetona.”


Sau ɗaya Allah ya faɗa, Sau biyu na ji, cewa Allah yake da iko.


Nakan shirya abin da zan yi, in kuwa yi shi. Ina da fahimi, ina da ƙarfi.


Kai babban mashawarci ne, mai aikata manyan ayyukanka. Kana ganin dukan ayyukan 'yan adam. Kakan sāka wa kowa bisa ga halinsa da ayyukansa.


Lalle ka fi Daniyel hikima, Ba asirin da yake ɓoye a gare ka.


Kada ka kai mu wurin jaraba, Amma ka cece mu daga Mugun.’


Ga wanda yake da iko yă tsare ku daga faɗuwa, yă kuma miƙa ku marasa aibi a gaban ɗaukakarsa da matuƙar farin ciki,


suna cewa da murya mai ƙarfi, “Macancanci ne Ɗan Ragon nan da aka yanka yă sami iko, da wadata, da hikima, da ƙarfi, da girma, da ɗaukaka, da yabo!”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan