Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 2:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Sai aka bayyana wa Daniyel asirin ta cikin wahayi da dare. Daga nan Daniyel ya yabi Allah na Sama.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 A wannan dare sai aka bayyana wa Daniyel mafarkin cikin wahayi. Daniyel kuwa ya ɗaukaka Allah na sama.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 2:19
16 Iomraidhean Croise  

Kamar wani irin mafarki mai razanarwa yake, Wanda ya hana ni jin daɗin barcina.


Ubangiji yakan amince da waɗanda suke biyayya da shi, Yakan koya musu alkawarinsa.


Waɗannan samari huɗu kuwa, Allah ya ba su ilimi, da sanin littattafai, da hikima. Ya kuma yi wa Daniyel baiwar ganewar wahayi da mafarkai.


Yana bayyana zurfafan abubuwa masu wuyar ganewa, Ya san abin da yake cikin duhu. Haske kuma yana zaune tare da shi.


Kamar yadda aka umarta a bar kututturen itacen da saiwoyinsa, haka nan za a tabbatar maka da sarautarka sa'ad da ka gane Mai Sama ne yake mulki.


‘Ya Belteshazzar shugaban masu sihiri, tun da yake na san ruhun alloli tsarkaka yana a cikinka, ba wani asirin da zai fi ƙarfin ganewarka. Ga mafarkin da na yi, sai ka faɗa mini fassararsa.


Daniyel ya ce, “A wahayi da dare na ga iskar samaniya daga kusurwa huɗu tana gurɓata babbar teku.


“Bayan wannan kuma a wahayi na dare na ga dabba ta huɗu mai ƙarfi ƙwarai, mai bantsoro da banrazana. Tana da haƙoran ƙarfe, zaga-zaga. Ta cinye, ta ragargaza, sa'an nan ta tattake sauran da ƙafafunta. Dabam take da sauran dabbobin da suka riga ta. Tana kuma da ƙaho goma.


Hakika Ubangiji ba yakan aikata kome ba, Sai da sanin bayinsa annabawa.


Ya ce, “Ku ji abin da zan faɗa! Idan akwai annabawa a cikinku, nakan bayyana gare su cikin wahayi, in kuma yi magana da su ta cikin mafarki.


Mutanen Isra'ila suka ji daɗin rahoton da aka ba su, suka yabi Allah, ba su sāke yin maganar zuwa yaƙi don su hallaka ƙasar da Ra'ubainawa da Gadawa suke zaune ba.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan