Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 2:12 - Littafi Mai Tsarki

12 Saboda haka sarki ya husata ƙwarai, ya umarta a karkashe duk masu hikima na Babila.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Wannan ya sa sarki ya fusata ƙwarai, ya ba da umarni a tafi da dukan masu hikima na Babilon a kashe su.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 2:12
14 Iomraidhean Croise  

Ba shi da amfani ka dami kanka Har ka mutu, saboda tsarguwa, gama wannan wawanci ne, Da aikin rashin hankali.


Hasalar mutane ba ta ƙara kome, sai dai ta ƙara maka yabo. Waɗanda suka tsira daga yaƙe-yaƙe za su kiyaye idodinka.


Mutum mai hikima yakan yi ƙoƙari ya faranta zuciyar sarki. Idan kuwa sarki ya hasala mai yiwuwa ne a kashe wani.


Hasalar sarki kamar rurin zaki ne, amma alherinsa kamar saukar ruwan sama ne.


Ka ji tsoron fushin sarki kamar yadda za ka ji tsoron zaki mai ruri, sa shi ya yi fushi kashe kai ne.


Mutum mai saurin fushi yakan ta da faɗa, mai zafin rai kuma yakan aikata laifi da yawa.


Sa'an nan Daniyel ya tafi wurin Ariyok wanda sarki ya sa ya karkashe masu hikima na Babila, ya ce masa, “Kada ka karkashe masu hikima na Babila, ka kai ni gaban sarki, ni kuwa zan yi wa sarki fassarar.”


Sai sarki ya amsa wa Kaldiyawa, ya ce, “Na mance da abin, idan ba ku tuno mini da mafarkin, duk da fassararsa ba, to, za a daddatse ku gunduwa gunduwa, a mai da gidajenku juji.


Nebukadnezzar fa, ya husata ya umarta a kawo Shadrak, da Meshak, da Abed-nego. Sai aka kawo su gaban sarki.


Sai Nebukadnezzar ya husata ƙwarai da Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, har fuskarsa ta sāke. Sai ya umarta a ƙara zuga wutar, har sau bakwai fiye da yadda take a dā.


Saboda girman da Allah ya ba shi, shi ya sa dukan jama'a, da al'ummai, da harsuna suka ji tsoronsa suka yi rawar jiki a gabansa. Bisa ga ganin damarsa yakan kashe wani, ya bar wani da rai, haka kuma yakan ɗaukaka wani, ya ƙasƙantar da wani.


Da Hirudus ya ga masanan nan sun mai da shi wawa, sai ya hasala ƙwarai, ya aika a karkashe dukan 'yan yara maza da suke Baitalami da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa ƙasa, gwargwadon lokacin da ya tabbatar a gun masanan nan.


Amma ni ina gaya muku, kowa yake fushi da ɗan'uwansa ma, za a hukunta shi. Kowa ya ce da ɗan'uwansa wawa, za a kai shi gaban majalisa. Kowa kuma ya ce, ‘Kai wofi!’ hakkinsa shiga Gidan Wuta.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan