Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 2:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Abin nan da sarki yake so a yi masa yana da wuya, ba wanda zai iya biya wa sarki wannan bukata, sai dai ko alloli waɗanda ba su zama tare da 'yan adam.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Abin da sarki yake nema yana da wuya matuƙa. Babu wani da zai iya bayyana wannan ga sarki sai dai alloli; kuma ba su zama tare da ’yan adam.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 2:11
25 Iomraidhean Croise  

Domin haka Fir'auna ya ce wa Yusufu, “Tun da yake Allah ya nuna maka waɗannan abu duka, ba wani mai basira da hikima kamarka,


Saboda haka da safe, hankalinsa ya tashi, sai ya aika aka kirawo dukan bokayen Masar da dukan masu hikimar Masar, Fir'auna kuwa ya faɗa musu mafarkansa, amma ba wanda ya iya fassara masa su.


“Amma ko Allah zai zauna a duniya? Ga shi, Saman sammai ba ta isa ta karɓe ka ba, balle wannan Haikali da na gina!


“Ashe kuwa Allah zai zauna tare da ɗan adam a duniya? Ga shi kuwa, sama da saman sammai ba su iya ɗaukarka ba, balle fa ɗakin da na gina.


“A nan zan zauna har abada. A nan kuma nake so in yi mulki.


Ya hau kan tsaunuka Tare da ɗumbun waɗanda ya kamo daga yaƙi, Yana karɓar kyautai daga wurin mutane, Daga wurin 'yan tawaye kuma. Ubangiji Allah zai zauna a can.


Zan zauna tare da Isra'ilawa, in zama Allahnsu.


Sai masu sihiri suka ce wa Fir'auna, “Ai, wannan aikin Allah ne.” Amma zuciyar Fir'auna ta taurare, har da bai kasa kunne ga Musa da Haruna ba, kamar yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.


Ki riƙe dukan sihirinki, da makarunki, da layunki, Kina amfani da su tun kina ƙarama. Watakila za su yi miki wani taimako, Watakila kya iya tsoratar da abokan gāba.


Gama haka wanda yake can Sama, Maɗaukaki, wanda ake kira Mai Tsarki ya ce, “Ina zaune a can Sama a tsattsarkan wuri, tare kuma da wanda yake da halin tuba mai tawali'u, don in farfaɗo da ruhun masu tawali'u, in kuma farfaɗo da zukatan masu tuba.


Ga ni tare da 'ya'yan da Ubangiji ya ba ni. Ubangiji Mai Runduna, wanda kursiyinsa a kan Dutsen Sihiyona yake, ya maishe mu rayayyen jawabi ga jama'ar Isra'ila.


“Ni, Nebukadnezzar ina cikin gidana, ina nishaɗi a fādata.


Ai, a cikin mulkinka akwai wani mutum wanda yake da ruhun alloli tsarkaka. A zamanin ubanka, an iske fahimi, da ganewa, da hikima irin na alloli a cikinsa. Sarki Nebukadnezzar ubanka, ya naɗa shi shugaban masu sihiri, da masu dabo, da bokaye, da masu duba.


Zan sāka alhakin jininsu, Ba zan kuɓutar da mai laifi ba, Gama Ubangiji yana zaune a Sihiyona.”


Kada ku ƙazantar da ƙasar da kuke zaune a ciki, wadda ni kuma nake zaune a ciki, gama ni Ubangiji ina zaune a tsakiyar jama'ar Isra'ila.”


Amma Yesu ya dube su, ya ce musu, “Ga mutane kam, ba mai yiwuwa ba ne, amma gun Allah kowane abu mai yiwuwa ne.”


Kalman nan kuwa ya zama mutum, ya zauna a cikinmu, yana mai matuƙar alheri da gaskiya. Mun kuma dubi ɗaukakarsa, ɗaukaka ce ta makaɗaicin Ɗa daga wurin Ubansa.


Shi ne Ruhu na gaskiya, wanda duniya ba ta iya samunsa, domin ba ta ganinsa, ba ta kuma san shi ba. Ku kam, kun san shi, domin yana zaune tare da ku, zai kuma kasance a zuciyarku.


Yesu ya amsa masa ya ce, “Kowa yake ƙaunata, zai kiyaye maganata, Ubana kuwa zai ƙaunace shi, za mu zo wurinsa mu zauna tare da shi.


Wace yarjejeniya ce take a tsakanin Haikalin Allah da gumaka? Domin mu haikali ne na Allah Rayayye. Yadda Allah ya ce, “Zan zauna tare da su, in yi yawo a tsakaninsu, Zan kuma kasance Allahnsu, Su kuma su kasance jama'ata.


Na kuma ji wata murya mai ƙara daga kursiyin, tana cewa, “Kun ga, mazaunin Allah na tare da mutane. Zai zauna tare da su, za su zama jama'arsa, Allah kuma shi kansa zai kasance tare da su,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan