Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 2:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Sa'an nan Kaldiyawa suka amsa wa sarki, suka ce, “Ba wani mahaluki a duniya wanda zai iya biyan wannan bukata ta sarki, gama ba wani sarki wanda ya taɓa yin irin wannan tambaya a wurin mai sihiri, ko mai dabo, ko Bakaldiye.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Sai masanan taurarin suka amsa wa sarki suka ce, “Babu wani mutum a duniyan nan da zai iya yin abin da sarki yake nema! Babu wani sarki mai daraja da girma wanda ya taɓa yin irin wannan tambaya ga masu sihiri ko masu dabo ko masanan taurari.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 2:10
5 Iomraidhean Croise  

Kome shawarar da kika samu ba ki da ƙarfi. Bari mashawartanki su fito su cece ki, Waɗancan mutane masu binciken taurari Waɗanda suka zana taswirar sammai, Su kuma faɗa miki Dukan abin da zai faru da yake wata wata.


Sai sarki ya umarta a kirawo masa masu sihiri, da masu dabo, da bokaye, da Kaldiyawa, su zo su fassara masa mafarkin da ya yi. Sai suka hallara a gaban sarki.


Daniyel ya amsa wa sarki, ya ce, “Ba masu hikima, ko masu dabo, ko masu sihiri, ko masu duba, da za su iya su warware wa sarki wannan matsala da ta dame shi.


A lokacin sai waɗansu Kaldiyawa suka tafi, suka yi ƙarar Yahudawa.


Sai masu sihiri, da masu dabo, da Kaldiyawa, da masu duba suka zo, na faɗa musu mafarkin, amma ba su iya yi mini fassararsa ba.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan