Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 12:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Sai ya ce, “Yi tafiyarka, Daniyel, gama an rufe wannan magana, an kuma kulle ta har ƙarshen lokaci.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Sai ya amsa ya ce, “Ka kama hanyarka, Daniyel, domin a rufe kalmomin aka kuma liƙe su har sai ƙarshen lokaci.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 12:9
8 Iomraidhean Croise  

Za a ɓoye muku ma'anar kowane annabci na cikin wahayi. Zai zama kamar naɗaɗɗen littafin da aka liƙe. Ko kun kai wa wanda ya iya karatu, don ya karanta muku, zai ce ba zai iya ba saboda a liƙe yake.


Almajiraina su ne za su lura, su kuma kiyaye jawabin da Allah ya ba ni.


Na zo ne don in ganar da kai a kan abin da zai faru da mutanenka nan gaba, gama wahayin yana a kan kwanaki na nan gaba ne.”


“A lokaci na ƙarshe sarkin kudu zai tasar masa, sarkin arewa kuwa zai tunzura, ya tasar masa da karusai da mahayan dawakai, da jiragen ruwa da yawa. Zai ratsa ƙasashe, ya ci su da yaƙi, ya wuce.


“Amma kai, Daniyel, sai ka rufe maganar, ka kuma kulle littafin, har zuwa ƙarshen lokaci. Mutane da yawa za su yi ta kai da kawowa, ilimi kuma zai ƙaru.”


Na ji, amma ban gane ba. Sai na ce, “Ya shugabana, mene ne ƙarshen waɗannan abubuwa?”


Wannan wahayi na kwanaki wanda aka nuna maka gaskiya ne, asiri ne kuma, kada ka faɗa, gama zai daɗe kafin a yi.”


Sa'ad da kuwa aradun nan bakwai suka yi tsawa, kamar zan rubuta, sai na ji wata murya daga sama tana cewa, “Rufe abin da aradun nan bakwai suka faɗa, kada ka rubuta.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan