Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 12:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Sai mutumin da yake sāye da rigar lilin ɗin, wanda yake tsaye a gaɓar kogin ya ɗaga hannuwansa sama, sa'an nan ya rantse da wanda yake rayayye har abada, ya ce, “Za a yi shekara uku da rabi. Za a kammala waɗannan abubuwa, sa'ad da aka gama ragargaje ikon tsarkakan mutane.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Mutumin da yake sanye da tufafin lilin, wanda yake a saman ruwan kogin, ya ɗaga hannun damansa da kuma na hagunsa sama, sai na ji yana rantsuwa da wannan da yake raye har abada, yana cewa, “Zai kasance na ɗan lokaci, lokuta da rabin lokaci. Za a kammala waɗannan abubuwa, sa’ad da aka gama ragargaje ikon tsarkakan mutane.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 12:7
30 Iomraidhean Croise  

“Na rantse da Allah Mai Iko Dukka, Wanda ya ƙwace mini halaliyata, Wanda ya ɓata mini rai.


Za a ce da ku, “Tsattsarkar Jama'ar Allah,” “Jama'ar da Ubangiji ya Fansa!” Za a kira Urushalima, “Birnin da Allah yake Ƙauna,” “Birnin da Allah bai Yashe shi Ba.”


Idan kun yi rantsuwa kuka ce, ‘Har da ran Ubangiji kuwa,’ Da gaskiya, da aminci, da adalci, Sa'an nan sauran al'umma za su so in sa musu albarka, Za su kuma yabe ni.”


Ka ce musu, ni Ubangiji Allah, na ce a ranar da na zaɓi Isra'ila na ta da hannuna, na rantse wa zuriyar Yakubu, na kuma bayyana kaina a gare su a ƙasar Masar, cewa ni ne Ubangiji Allahnsu,


Da na ɗaga kaina sai na ga wani sāye da rigar lilin, ya ɗaura ɗamara ta zinariya tsantsa.


Sarkin arewa kuwa zai tara babbar rundunar soja fiye da ta dā. Bayan waɗansu shekaru kuwa zai kama hanya da babbar rundunar soja, da kayan faɗa masu yawan gaske.


Dayansu ya ce wa mutumin da yake sāye da rigar lilin, wanda yake tsaye a gaɓar kogin, “Sai yaushe waɗannan abubuwan banmamaki za su ƙare?”


Na ji, amma ban gane ba. Sai na ce, “Ya shugabana, mene ne ƙarshen waɗannan abubuwa?”


Kafin sarki ya rufe baki sai ga murya daga sama, tana cewa, “Ya sarki Nebukadnezzar, da kai ake magana, yanzu an tuɓe ka daga sarauta.


“A ƙarshen kwanakin, sai ni Nebukadnezzar, na ɗaga ido sama, sai hankalina ya komo mini, na ɗaukaka Maɗaukaki, na yabe shi, na girmama shi wanda yake rayayye har abada. “Gama mulkinsa madawwamin mulki ne, Sarautarsa kuwa daga zamani zuwa zamani.


“Ina dubawa ke nan sai ga wannan ƙaho yana yaƙi da tsarkaka har ya rinjaye su,


Zai yi maganganun saɓo a kan Maɗaukaki, zai tsananta wa tsarkaka na Maɗaukaki, zai yi ƙoƙari ya sāke lokatai, da shari'a, za a kuwa bashe su a hannunsu, har shekara uku da rabi.


Ya ce mini, “Sai an yi kwana dubu biyu da ɗari uku, sa'an nan za a mai da wuri mai tsarki daidai da yadda yake a dā.”


Zai ƙasaita, amma ba ta wurin ikon kansa ba. Zai yi mummunar hallakarwa. Zai hallaka manyan mutane, da tsarkaka. Zai yi nasara cikin abin da zai yi.


Saboda haka, sai ku ƙudura a ranku, a kan ba za ku damu da yadda za ku mai da jawabi ba.


Za a kashe waɗansu da kaifin takobi, a kuma kakkama waɗansu a kai su bauta zuwa ƙasashen al'ummai duka. Al'ummai kuma za su tattake Urushalima, har ya zuwa cikar zamaninsu.”


Shi kuwa zai ɗaukaka ku ku zama abin yabo, masu suna, masu daraja, fiye da dukan al'umman da ya yi. Za ku zama jama'a tsattsarka ta Ubangiji Allahnku kamar yadda ya faɗa.”


Ubangiji zai ɗauka wa jama'arsa fansa, Zai ji ƙan bayinsa, Sa'ad da ya ga ƙarfinsu ya kāsa, Ba kuma wanda ya ragu, bawa ko ɗa.


Na ɗaga hannuna sama, Na rantse da madawwamin raina,


Gama ku jama'a ce tsattsarka ta Ubangiji Allahnku. Ubangiji Allahnku ya zaɓe ku daga cikin dukan al'ummai don ku zama jama'arsa, abar mulkinsa.


Amma ku kabila ce zaɓaɓɓiya, ƙungiyar firistocin babban Sarki, tsattsarkar al'umma, jama'ar mallakar Allah, domin ku sanar da mafifitan al'amuran wannan da ya kirawo ku daga cikin duhu, kuka shiga maɗaukakin haskensa.


Amma aka ba matar fikafikan nan biyu na babban juhurman nan, don ta tashi ta guje wa macijin nan, ta shiga jeji, ta je wurin da za a cishe ta a lokaci ɗaya, da lokatai, da rabin lokaci.


Matar kuwa, sai ta gudu ta shiga jeji, a inda Allah ya shirya mata wurin da za a cishe ta har kwana dubu da metan da sittin.


An kuwa ba dabbar nan baki, tana fariya da maganganun saɓo, aka kuma yardar mata ta zartar da iko, har wata arba'in da biyu.


sai dattawan nan ashirin da huɗu suka fāɗi a gaban wanda yake a zaune a kan kursiyin, su yi masa sujada, shi da yake a raye har abada abadin, su kuma ajiye kambinsu a gaban kursiyin, suna waƙa, suna cewa,


Duk lokaci kuma da rayayyun halittan nan suka ɗaukaka wanda yake zaune a kan kursiyin, yake kuma raye har abada abadin, suka girmama shi, suka kuma gode masa,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan