Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 12:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Dayansu ya ce wa mutumin da yake sāye da rigar lilin, wanda yake tsaye a gaɓar kogin, “Sai yaushe waɗannan abubuwan banmamaki za su ƙare?”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Ɗayansu ya ce wa mutumin da yake sanye da tufafin lilin, wanda yake a saman ruwan kogin, “Har yaushe waɗannan abubuwan banmamakin za su cika?”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 12:6
16 Iomraidhean Croise  

Ba sauran tsarkakan alamu, Ba sauran annabawan da suka ragu, Ba kuwa wanda ya san ƙarewar wannan.


Sai ga mutum shida sun taho daga wajen ƙofa wadda take daga bisa wadda ta fuskanci arewa. Kowa yana da makaminsa na kisa a hannu. Tare da su kuma akwai wani mutum saye da rigar lilin, yana kuma rataye da gafaka. Sai suka tafi suka tsaya a gefen bagaden tagulla.


Sa'an nan ni Daniyel na duba, sai ga waɗansu biyu a tsaye, ɗaya a wannan gāɓa ɗayan kuma a waccan gāɓar kogin.


Na ji, amma ban gane ba. Sai na ce, “Ya shugabana, mene ne ƙarshen waɗannan abubuwa?”


Sai na ji wani mai tsarki yana magana, wani kuma mai tsarki ya tambayi wancan mai tsarki da ya yi magana, ya ce, “Sai yaushe za a tsai da abubuwan da suke a wahayin nan, wato hana yin hadayar ƙonawa ta yau da kullum, da zunubin da yake lalatarwa, da ba da wuri mai tsarki ga rundunar mutane don a tattake?”


Na kuma ji muryar mutum a gāɓar Ulai ta ce, “Jibra'ilu, ka sa wannan mutum ya gane wahayin.”


Yana zaune a kan Dutsen Zaitun sai almajiransa suka zo wurinsa a kaɗaice, suka ce, “Gaya mana, yaushe za a yi waɗannan abubuwa? Mece ce kuma alamar dawowarka, da ta ƙarewar zamani?”


“Gaya mana yaushe za a yi waɗannan abubuwa? Wace alama kuma za a gani sa'ad da suke shirin aukuwa?”


An yi wannan ne kuwa domin a yanzu a sanar da hikimar Allah iri iri ga manyan mala'iku da masu iko a samaniya, ta hanyar Ikkilisiya.


An dai bayyana musu, cewa ba kansu suke bauta wa ba, ku suke bauta wa, a game da abubuwan da masu yi muku bishara, ta ikon Ruhu Mai Tsarki, wanda aka aiko daga sama suka samar da ku a yanzu. Su ne kuwa abubuwan da mala'iku suke ɗokin gani.


Sai mala'ika bakwai ɗin nan masu bala'i bakwai suka fito daga Haikalin, saye da tufafin lilin mai tsabta, mai ɗaukar iko, da ɗamarar zinariya a ƙirjinsu.


Rundunonin Sama, saye da lallausan lilin fari mai tsabta, suna a biye da shi a kan fararen dawakai.


Sai suka ta da murya da ƙarfi suka ce, “Ya Ubangiji Mamallaki, Mai Tsarki, Mai Gaskiya, sai yaushe ne za ka yi hukunci, ka ɗaukar mana fansar jininmu a gun mazaunan duniya?”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan