Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 12:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Waɗanda suke da hikima za su haskaka kamar sararin sama, waɗanda kuma suka juyar da mutane da yawa zuwa adalci, za su zama kamar taurari har abada abadin.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Waɗanda suke da hikima za su haskaka kamar hasken samaniya, waɗanda kuma suka jagoranci waɗansu da yawa zuwa adalci, za su zama kamar taurari har abada abadin.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 12:3
27 Iomraidhean Croise  

Jama'ar Isra'ila kuwa sukan ga fuskar Musa tana annuri. Sa'an nan Musa ya sāke lulluɓe fuskarsa, har lokacin da ya shiga don ya yi magana da Ubangiji.


Adalci yana rayar da mutum, wanda yake da hikima kuma yakan ceci rayuka.


Mutane masu hikima za su sami kyakkyawan suna, amma wawaye sukan ƙara wa kansu shan kunya.


Hanyar da adalai suke bi kamar fitowar rana ce, sai ta yi ta ƙara haske, har ta take tsaka.


Saboda hikimar Mai Hadishi ya koya wa mutane ilimi. Ya auna, ya bincika, ya tsara karin magana da lura sosai.


Bayan shan wahalarsa, zai sāke yin murna, Zai fahimta wahalar da ya sha ba ta banza ba ce, Shi ne bawana, adali, Zai ɗauki hukuncin mutane masu yawa, Ya sa su zama mutanena amintattu.


Amma da a ce sun tsaya cikin shawarata, Da sun yi shelar maganata ga jama'ata, Da sun juyar da su daga muguwar hanyarsu, Da mugayen ayyukansu.


Waɗansu daga cikin mutane waɗanda suke da hikima, za su wayar da kan mutane da yawa. Amma duk da haka za a kashe su da takobi, waɗansu da wuta, a washe waɗansu a kai su bauta.


Waɗanda suke da hikima, za a kāshe su, don a tsabtace su, a tsarkake su, su yi tsab tsab, har matuƙar da aka ƙayyade ta yi.


Mutane da yawa za su tsarkake kansu, su zama masu tsabta tsab tsab, amma mugaye ba za su gane ba, za su yi ta muguntarsu, amma masu hikima za su gane.


Sa'an nan ne masu adalci za su haskaka kamar rana a Mulkin Ubansu. Duk mai kunnen ji, yă ji.”


Yesu ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, a sabon zamani, sa'ad da Ɗan Mutum ya zauna a maɗaukakin kursiyinsa, ku da kuka bi ni, ku ne kuma za ku zauna a kursiyi goma sha biyu, kuna hukunta kabilan nan goma sha biyu na Isra'ila.


“Wane ne amintaccen bawan nan mai hikima, da ubangidansa ya ba shi riƙon gidansa, yă riƙa ba su abincinsu a kan kari?


Mai girbi na samun lada, yana kuma tara amfani zuwa rai madawwami, domin mai shuka da mai girbi su yi farin ciki tare.


Yahaya fitila ne mai ci, mai haske kuma, kun kuwa yarda ku yi farin ciki matuƙa da haskensa ɗan lokaci kaɗan.


To, a Ikkilisiyar da take Antakiya akwai waɗansu annabawa, da masu koyarwa, wato Barnaba, da Saminu wanda ake kira Baƙi, da Lukiyas Bakurane, da Manayan wanda aka goya tare da sarki Hirudus, da kuma Shawulu.


Kamar gwanin magini, haka na sa harsashin gini, gwargwadon baiwar alherin da Allah ya yi mini, wani kuma yana ɗora gini a kai. Sai dai kowane mutum, yă lura da irin ginin da yake ɗorawa a kai.


Ya kuma yi wa waɗansu baiwa su zama manzanni, waɗansu annabawa, waɗansu masu yin bishara, waɗansu makiyaya masu koyarwa,


Ko da yake kamar a yanzu kam, ai, ya kamata ku zama masu koyarwa, duk da haka, ashe, ba ku wuce wani ya sāke koya muku jigajigan farko na Maganar Allah ba, har ya zamana sai an ba ku nono, ba abinci mai tauri ba.


Ku ɗauki haƙurin Ubangijinmu, ceto ne. Haka ma, ƙaunataccen ɗan'uwanmu Bulus ya rubuto muku, bisa ga hikimar da aka ba shi,


Asirtacciyar ma'anar taurarin nan bakwai da ka gani a hannuna na dama kuwa, da kuma fitilun nan bakwai na zinariya, to, su taurarin nan bakwai, mala'iku ne na ikilisiyoyin nan bakwai, fitilun nan bakwai kuwa, ikkilisiya bakwai ɗin ne.


Ta haka, ya Ubangiji ka sa maƙiyanka su mutu, Amma abokanka su haskaka kamar fitowar rana! Ƙasar kuwa ta zauna lafiya shekara arba'in.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan