Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 12:13 - Littafi Mai Tsarki

13 “Ka yi tafiyarka ka huta, a ƙarshen kwanaki za ka tashi ka karɓi naka rabo.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 “Gare ka dai, ka yi tafiyarka har zuwa ƙarshe. Za ka huta, sa’an nan a ƙarshen kwanaki za ka tashi don karɓi sashen gadon da aka ba ka.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 12:13
16 Iomraidhean Croise  

Allah kuwa zai hukunta mugaye, Masu zunubi kuwa za a ware su daga adalai.


Kai ne kaɗai, nake da shi, ya Ubangiji, Kai ne kake biyan dukan bukatata, Raina yana hannunka.


Don haka cike nake da murna da farin ciki, Kullum kuwa ina jin kome lafiya yake,


Ubangiji kuwa ya ce, “Zan tafi tare da kai, zan kuma hutashe ka.”


Waɗanda suke da hikima za su haskaka kamar sararin sama, waɗanda kuma suka juyar da mutane da yawa zuwa adalci, za su zama kamar taurari har abada abadin.


“Amma kai, Daniyel, sai ka rufe maganar, ka kuma kulle littafin, har zuwa ƙarshen lokaci. Mutane da yawa za su yi ta kai da kawowa, ilimi kuma zai ƙaru.”


“Ubangiji Mai Runduna ya ce, ‘Idan ka yi tafiya a hanyata, ka kuma kiyaye umarnina, zan sa ka zama shugaban Haikalina, ka lura da shirayina, zan kuma sa ka sami damar zuwa wurin waɗannan da yake tsaye.


Yesu ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, a sabon zamani, sa'ad da Ɗan Mutum ya zauna a maɗaukakin kursiyinsa, ku da kuka bi ni, ku ne kuma za ku zauna a kursiyi goma sha biyu, kuna hukunta kabilan nan goma sha biyu na Isra'ila.


Koyaushe ku zauna a faɗake, kuna addu'a ku sami ikon tsere wa dukan waɗannan al'amura da za su auku, ku kuma tsaya a gaban Ɗan Mutum.”


Gama mun sani in an rushe jikinmu na wannan duniya, Allah ya tanadar mana jiki a Sama, wato, wanda shi kansa ya yi, wanda zai dawwama.


yă kuma ba ku hutu har da mu ma, ku da ake ƙuntata wa ɗin, a ranar bayyanar Ubangiji Yesu daga Sama tare da manyan mala'ikunsa, a cikin wuta mai ruruwa,


Sai kuma na ji wata murya daga Sama tana cewa, “Rubuta wannan. Albarka tā tabbata ga matattu, wato, waɗanda za su mutu a nan gaba a kan su na Ubangiji ne.” Ruhu ya ce, “Hakika, masu albarka ne, domin su huta daga wahalarsu, gama aikinsu yana a biye da su!”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan