Daniyel 12:12 - Littafi Mai Tsarki12 Masu farin ciki ne waɗanda suka daure, har suka kai ƙarshen kwana dubu da ɗari uku da talatin da biyar. Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 202012 Mai albarka ne wanda ya jira har yă zuwa ƙarshen kwanakin nan 1,335. Faic an caibideil |
Sa'an nan na ga kursiyai, da waɗanda aka bai wa ikon hukunci, zaune a kai. Har wa yau, kuma na ga rayukan waɗanda aka fille wa kai saboda shaidar da suka yi wa Yesu, da kuma Maganar Allah, ba su kuwa yi wa dabbar nan da siffarta sujada ba, ba su kuma yarda a yi musu alamarta a goshinsu ko a hannunsu ba, sun sāke rayuwa, sun yi mulki tare da Almasihu har shekara dubu.