Daniyel 12:1 - Littafi Mai Tsarki1 “A wannan lokaci Mika'ilu babban shugaba wanda yake lura da jama'arka zai bayyana. A lokacin za a yi tashin hankali irin wanda ba a taɓa yi ba, tun da aka yi duniya. Amma a lokacin za a ceci jama'arka waɗanda aka rubuta sunayensu cikin littafi. Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 20201 “A wannan lokaci Mika’ilu, babban mai mulki wanda yake kāre mutanenka, zai tashi. Za a yi lokacin matsananciyar wahala wanda ba a taɓa yi tun farkon ƙasashe har zuwa yanzu. Amma a lokacin da mutanenka, kowane mutum wanda aka sami sunansa a rubuce a cikin littafin, za a cece shi. Faic an caibideil |