Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 11:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Zai kwashe gumakansu ganima, da siffofinsu na zubi, ya kai Masar, tare da tasoshinsu na azurfa da na zinariya masu daraja. Zai yi shekaru bai kai wa sarkin arewa yaƙi ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Zai ƙwace allolinsu, siffofinsu na ƙarfe da kuma kaya masu daraja na azurfa da na zinariya a kuma kai su Masar. Zai yi ’yan shekaru bai kai wa sarkin Arewa yaƙi ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 11:8
17 Iomraidhean Croise  

Amma yanzu, ka gudu domin kana kewar gidan mahaifinka ƙwarai, amma don me ka sace mini gumakana?”


Filistiyawa suka gudu, suka bar gumakansu a nan, Dawuda da mutanensa suka kwashe su.


A daren nan zan ratsa ƙasar Masar, in bugi kowane ɗan fari na ƙasar, na mutum da na dabba. Zan hukunta gumakan Masar duka, gama ni ne Ubangiji.


Zai nutsar da jiragen ruwa mafi girma mafi kyau.


suka ƙaƙƙone gumakansu waɗanda ba Allah ba ne ko kaɗan, siffofi ne kurum na itace da na dutse, da mutane suka yi da hannuwansu.


Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, “Ga shi, zan hukunta Amon na No, da Fir'auna, da Masar, tare da allolinta, da sarakunanta, wato Fir'auna, tare da waɗanda suke dogara gare shi.


A makon nan uku ban ci wani abincin kirki ba, balle nama ko shan ruwan inabi, ban kuma shafa mai ba.


Bayan wannan sarkin arewa zai kai wa sarkin kudu yaƙi, amma tilas zai janye, ya koma ƙasarsa.


Ko da yake Isra'ila tana bunƙasa kamar ciyayi, Iskar gabas, wato iskar da za ta zo daga jeji, Za ta busar da maɓuɓɓugarsu da idon ruwansu, Za ta lalatar da abubuwa masu amfani da yake cikin taskarsu.


Ai, mai aikin hannu ne ya yi shi a Isra'ila! Gunki ne ba Allah ba ne. Za a farfashe siffar maraƙin Samariya.


Masarawa suna ta binne gawawwakin 'ya'yan farinsu da Ubangiji ya karkashe musu. Banda 'ya'yan farinsu kuma Ubangiji ya hukunta wa allolinsu.


Sai ku rurrushe bagadansu, ku ragargaje al'amudansu, ku ƙone ginshiƙansu na tsafi, ku kuma sassare siffofin gumakansu, ku shafe sunayensu daga wuraren nan.


Mika kuwa ya ce musu, “Kun kwashe allolina da na yi, da firist ɗina, me ya rage mini kuma? Sa'an nan ku ce mini, ‘Me ya faru?’ ”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan