Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 11:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Ba za a daɗe ba, wani daga cikin danginta zai tasar wa sojojin sarkin arewa da yaƙi, ya shiga kagararsu, ya ci su da yaƙi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 “Wani daga cikin zuriyarta zai taso yă ɗauki matsayinta. Zai kai wa sojojin sarkin Arewa hari yă kuma shiga kagararsa; zai yi yaƙi da su yă kuma yi nasara.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 11:7
14 Iomraidhean Croise  

“Akwai sa zuciya ga itacen da aka sare, Yana iya sāke rayuwa ya yi toho.


Ka aukar masa da ajalinsa nan da nan, Ka sa wani ya ɗauki matsayinsa!


Amma kai, ya Allah, za ka jefar da masu kisankai, da maƙaryata can ƙasa cikin zurfafa, Kafin su kai rabin kwanakinsu a duniya. Amma ni, zan dogara gare ka.


Gidan sarautar Dawuda kamar itacen da aka sare ne, amma kamar yadda rassa sukan toho daga cikin kututture, haka nan za a sami sabon sarki daga zuriyar Dawuda.


A rana ɗaya Ubangiji zai hukunta shugabannin Isra'ila da jama'arta. Zai hallaka kawunansu da ƙafafunsu, da dabino da iwa,


Kai ka dasa su, sun kuwa yi saiwa, Suna girma, suna kuma ba da 'ya'ya, Sunanka na a cikin bakinsu, amma kana nesa da zuciyarsu.


Bai kuwa cika rantsuwarsa da alkawarinsa ba. Ya ƙulla alkawari, amma ga shi, ya aikata dukan waɗannan abubuwa, ba zai kuɓuta ba.


“A lokaci na ƙarshe sarkin kudu zai tasar masa, sarkin arewa kuwa zai tunzura, ya tasar masa da karusai da mahayan dawakai, da jiragen ruwa da yawa. Zai ratsa ƙasashe, ya ci su da yaƙi, ya wuce.


Bayan waɗansu shekaru za su ƙulla zumunci. Sarkin kudu zai aurar wa sarkin arewa da 'yarsa don sāda zumunci, amma ba za ta sami iko ba. Shi da zuriyarsa ba za su amince da ita ba. Za a yi watsi da ita, ita da masu yi mata hidima, da mahaifinta, da waliyyinta.


“Duba rana tana zuwa, sa'ad da dukan masu girmankai, da mugaye za su ƙone kamar tattaka, a ran nan za su ƙone ƙurmus ba abin da zai ragu, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.


Amma Allah ya ce masa, ‘Kai marar azanci! A daren nan za a karɓi ranka. To, kayan da ka tanada, na wa za su zama?’


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan