Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 11:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Bayan waɗansu shekaru za su ƙulla zumunci. Sarkin kudu zai aurar wa sarkin arewa da 'yarsa don sāda zumunci, amma ba za ta sami iko ba. Shi da zuriyarsa ba za su amince da ita ba. Za a yi watsi da ita, ita da masu yi mata hidima, da mahaifinta, da waliyyinta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Bayan ’yan shekaru, za su haɗa kai. Diyar sarkin Kudu za tă je wurin sarkin Arewa ta sada zumunci, amma ba za tă riƙe iko ba, shi kuwa da ikonsa ba za su daɗe ba. A waɗannan kwanaki za a bashe ta, da ita da masu rakiyarta da kuma mahaifinta da kuma wanda ya goyi bayanta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 11:6
9 Iomraidhean Croise  

Akan hana wa mugaye haske, Sa'ad da sukan ɗaga hannuwansu sama akan kakkarya su.


Yakan yi nasara a dukan abin da yake yi. Ba zai fahimci hukuncin Allah ba, Yana yi wa abokan gābansa duban raini.


“Ɗan mutum, na karya hannun Fir'auna, Sarkin Masar, ga shi, ba za a ɗora hannun ba, don kada ya warke ya zama da ƙarfi yadda zai iya riƙon takobi.”


Sarkin arewa kuwa zai tara babbar rundunar soja fiye da ta dā. Bayan waɗansu shekaru kuwa zai kama hanya da babbar rundunar soja, da kayan faɗa masu yawan gaske.


Sa'an nan sarkin arewa zai zo ya gina mahaurai a jikin garun birni don ya ci birnin da yaƙi. Sojojin kudu kuwa ba za su iya tsayawa ba, ko zaɓaɓɓun jarumawansa ma, gama za su rasa ƙarfin tsayawa.


“A lokaci na ƙarshe sarkin kudu zai tasar masa, sarkin arewa kuwa zai tunzura, ya tasar masa da karusai da mahayan dawakai, da jiragen ruwa da yawa. Zai ratsa ƙasashe, ya ci su da yaƙi, ya wuce.


Ba za a daɗe ba, wani daga cikin danginta zai tasar wa sojojin sarkin arewa da yaƙi, ya shiga kagararsu, ya ci su da yaƙi.


Gama ga shi, zan sa wani makiyayi a ƙasan nan, wanda ba zai kula da masu lalacewa ba, ko waɗanda suka warwatse, ko ya warkar da gurgu, ko ya ciyar da waɗanda suka ragu, amma zai ci naman masu ƙiba, ya farfashe kofatonsu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan