Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 11:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Sa'ad da ya ƙasaita mulkinsa zai faɗi, a rarraba shi kashi huɗu a ba waɗansu waɗanda ba zuriyarsa ba, amma ba za su yi mulki da iko kamar yadda ya yi ba, gama za a tumɓuki mulkinsa saboda waɗansu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Bayan da ya bayyana, daularsa za tă wargaje za a rarraba ta zuwa kusurwoyi huɗu na duniya, a ba waɗansu waɗanda ba zuriyarsa ba, ba kuwa za su yi mulki da iko kamar yadda ya yi ba, gama za a tumɓuki daularsa a kuma ba wa waɗansu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 11:4
24 Iomraidhean Croise  

Bai kuma fi inuwa ba! Duk abin da yake yi banza ne, Yakan tara dukiya, amma bai san wanda zai more ta ba!


mutumin da ba shi da kowa, ba ɗa, ba ɗan'uwa, duk da haka a kullum yana ta fama da aiki. Bai taɓa ƙoshi da wadatar da yake da ita ba. Saboda me yana ta fama da aiki, ya hana wa kansa jin daɗi? Wannan ma aikin banza ne, zaman baƙin cikin ne.


Bayan na tumɓuke su kuma, zan sāke yi musu jinƙai, in komar da su, kowanne zuwa gādonsa.


Amma idan wata al'umma za ta ƙi kasa kunne, to, sai in tumɓuke ta ɗungum, in hallaka ta, in ji Ubangiji.”


A duk lokacin da na ce zan tumɓuke, in kakkarya in hallaka wata al'umma, ko wani mulki,


Dukan filin kwarin gawawwaki da toka, da dukan filaye har zuwa rafin Kidron zuwa kan kusurwar Ƙofar Doki wajen gabas, za su zama mai tsarki ga Ubangiji. Ba za a ƙara tumɓuke shi ko a rushe shi ba har abada.”


“Sai ka faɗa wa Baruk cewa, ‘Ni Ubangiji na ce, ga shi, abin da na gina zan rushe shi, abin da kuma na dasa zan tumɓuke shi, wato ƙasar ɗungum.


Zan sa iska ta hura a kan Elam daga kusurwoyi huɗu na samaniya. Za ta watsar da mutane ko'ina, Har ba ƙasar da za a rasa mutumin Elam a ciki.


Sa'an nan Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum, ka yi annabci a kan iska, ka ce mata, ni Ubangiji Allah na ce ta zo daga kusurwa huɗu, ta hura a kan waɗannan matattu domin su rayu.”


Daniyel ya ce, “A wahayi da dare na ga iskar samaniya daga kusurwa huɗu tana gurɓata babbar teku.


“Bayan wannan kuma, sai ga wata dabba mai kama da damisa tana da fikafikai huɗu irin na tsuntsu a bayanta, tana kuma da kai huɗu. Sai aka ba ta mulki.


Ina duban ƙahonin, sai ga wani ƙaho, ɗan ƙanƙane, ya ɓullo a tsakiyarsu. Sai aka tumɓuke ƙaho uku na fari daga cikinsu. Wannan ƙaramin ƙaho yana da idanu kamar na mutum, yana kuma da baki, yana hurta maganganu na fariya.”


Ƙahoni huɗu da suka tsiro bayan karyewar na farin, sarakuna huɗu ne da za su fito daga cikin al'ummarsa, amma ba za su sami iko irin nasa ba.


Sa'an nan bunsurun ya ɗaukaka kansa ƙwarai, amma sa'ad da ya ƙasaita sai babban ƙahon nan ya karye, a maimakonsa sai waɗansu ƙahoni huɗu na gaske suka tsiro suna fuskantar kusurwa huɗu.


Ubangiji ya ce, “Yanzu ku gudu daga ƙasar arewa, gama na warwatsa ku a waje kamar iska ta kusurwoyi huɗu na duniya!


Ya ce mini, “Waɗannan su ne ruhohi huɗu waɗanda suka fito daga sama bayan da sun nuna kansu a gaban Ubangijin duniya duka.


Da yake Yesu ya san tunaninsu, sai ya ce musu, “Duk mulkin da ya rabu a kan gāba, zai lalace. Ba kuma gari ko gidan da ya rabu a kan gāba, yă ɗore.


Amma Allah ya ce masa, ‘Kai marar azanci! A daren nan za a karɓi ranka. To, kayan da ka tanada, na wa za su zama?’


Bayan wannan na ga mala'iku huɗu, a tsaye a kusurwa huɗu ta duniya, suna tsare da iskokin nan huɗu na duniya, don kada wata iska ta busa a kan ƙasa, ko a kan teku, ko a kan wani itace.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan