Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 11:38 - Littafi Mai Tsarki

38 A maimakon haka zai girmama gunkin kagarai, gunkin da kakanninsa ba su ko sani ba, shi ne zai miƙa masa zinariya, da azurfa, da duwatsu masu daraja, da abubuwa masu tamani.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

38 A maimakonsu, zai ɗaukaka allahn kagarai; allahn da kakanninsa ba su ko sani ba, shi ne zai miƙa masa zinariya, da azurfa, da duwatsu masu daraja, da abubuwa masu tsada.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 11:38
8 Iomraidhean Croise  

Dukan waɗanda suke ƙera gumaka mutanen banza ne, gumakan da suke sa wa kuɗi da tsada kuma aikin banza ne. Waɗanda suke yi wa gumaka sujada kuwa makafi ne su, jahilai, za su sha kunya.


Ba zai kula da gumakan kakanninsa ba, ko begen da mata suke yi. Ba kuwa zai kula da kowane irin gunki ba, domin zai aza kansa ya fi su duka.


Zai tasar wa kagara mafi ƙarfi da taimakon baƙon gunki. Waɗanda suka yarda da shi, zai ba su girma, ya kuma shugabantar da su a kan mutane da yawa, zai raba musu ƙasa ta zama ladansu.


Ba za a daɗe ba, wani daga cikin danginta zai tasar wa sojojin sarkin arewa da yaƙi, ya shiga kagararsu, ya ci su da yaƙi.


To, Ruhu musamman ya ce, a can wani zamani waɗansu za su fanɗare wa bangaskiya, su mai da hankali ga aljannu masu ruɗi, da kuma koyarwar aljannu,


wato, zinariya, da azurfa, da duwatsun alfarma, da lu'ulu'u, da lallausan lilin, da hajja mai ruwan jar garura, da siliki, da jan alharini, da itacen ƙanshi iri iri, da kayan hauren giwa iri iri, da kayan da aka sassaƙa da itace mai tsada, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na dutse mai sheƙi,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan