Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 11:36 - Littafi Mai Tsarki

36 “Sa'an nan sarki zai yi yadda ya ga dama. Zai ɗaukaka kansa, ya aza ya fi kowane allah. Zai kuma yi maganganu na saɓo a kan Allahn alloli, zai yi nasara, sai lokacin da aka huce haushi, gama abin da aka ƙaddara zai cika.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

36 “Sarkin zai yi abin da ya ga dama. Zai ɗaukaka yă kuma girmama kansa gaba da kowane allah zai kuma faɗa munanan abubuwa a kan Allahn alloli. Zai yi nasara har sai lokacin hukunci ya cika, gama abin da aka ƙaddara zai cika.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 11:36
47 Iomraidhean Croise  

Ku gode wa Allahn da ya fi dukan alloli girma, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.


Ubangiji yakan sassoke manufofin sauran al'umma, Yakan hana su aikata shirye-shiryensu.


Mutum ya iya shirya dabaru iri iri, amma sai nufin Ubangiji ne zai tabbata.


Hakika a ƙasar duka, Ubangiji Allah Mai Runduna zai kawo hallaka kamar yadda ya ce zai yi.


Saura kaɗan in gama hukuncin da nake yi muku, sa'an nan in hallaka su.


Ubangiji ya ce, “Assuriya! Ina yin amfani da Assuriya kamar kulki don in hukunta waɗanda nake fushi da su.


Ka yi niyyar hawan sama, ka sa gadon sarautarka a kan taurari mafi nisa. Ka zaci za ka zauna kamar sarki a kan dutsen nan na arewa, inda alloli suke tattare.


Kai ka ce za ka hau can bisa kan taurari, ka zama kamar Mai Iko Dukka.


Jama'ata, ku shiga gidajenku, ku kukkulle ƙofofi, ku ɓoye kanku ɗan lokaci, kafin Allah ya huce daga fushinsa.


An riga an shirya wurin ƙonawa don Sarkin Assuriya. An tsiba itace cike da wurin. Kamar kibritu, numfashin Ubangiji zai cinna masa wuta.


Tun da farko na faɗa muku yadda abin zai zama, Tuntuni na yi faɗi a kan abin da zai faru. Na kuwa ce shirye-shiryena ba za su taɓa fāɗuwa ba, Zan aikata dukan abin da na yi niyyar yi.


Kun tafi wurin Molek da mai, da turare iri iri da kuka riɓaɓɓanya. Kun aika jakadunku can nesa, kun aike su su gangara, har zuwa lahira.


“Dan mutum, ka faɗa wa Sarkin Taya, cewa Ubangiji Allah ya ce, “ ‘Da yake zuciyarka ta cika da alfarma, Har ka ce kai allah ne, Kana zaune a mazaunin allah, kana zaune a tsakiyar tekuna, To, kai mutum ne kawai, ba allah ba, Ko da yake ka aza kanka mai hikima ne kamar Allah.


Na ji tsiwa da dukan surutan da ya yi mini.


Amma wanda ya kawo masa yaƙin zai yi yadda ya ga dama, ba wanda zai iya ja da shi. Zai tsaya a ƙasa mai albarka, ya mallake ta duka.


“Sa'an nan wani sarki babba zai taso wanda zai yi mulki da babban iko yadda ya ga dama.


Ba zai kula da gumakan kakanninsa ba, ko begen da mata suke yi. Ba kuwa zai kula da kowane irin gunki ba, domin zai aza kansa ya fi su duka.


Sai mutumin da yake sāye da rigar lilin ɗin, wanda yake tsaye a gaɓar kogin ya ɗaga hannuwansa sama, sa'an nan ya rantse da wanda yake rayayye har abada, ya ce, “Za a yi shekara uku da rabi. Za a kammala waɗannan abubuwa, sa'ad da aka gama ragargaje ikon tsarkakan mutane.”


Ya kuma ce wa Daniyel, “Hakika, Allahnka, Allahn alloli ne da Ubangijin sarakuna, mai bayyana asirai, gama ka iya bayyana wannan asiri.”


Dukan mazaunan duniya ba a bakin kome suke a gare shi ba. Yakan yi yadda ya nufa da rundunar sama da mazaunan duniya, Ba mai hana shi, ba kuma mai ce masa, ‘Me kake yi?’


Saboda girman da Allah ya ba shi, shi ya sa dukan jama'a, da al'ummai, da harsuna suka ji tsoronsa suka yi rawar jiki a gabansa. Bisa ga ganin damarsa yakan kashe wani, ya bar wani da rai, haka kuma yakan ɗaukaka wani, ya ƙasƙantar da wani.


Amma sa'ad da ya kumbura, ya taurare ransa yana ta yin girmankai, sai aka kore shi daga gadon sarautarsa, aka raba shi kuma da darajarsa.


Ina duban ƙahonin, sai ga wani ƙaho, ɗan ƙanƙane, ya ɓullo a tsakiyarsu. Sai aka tumɓuke ƙaho uku na fari daga cikinsu. Wannan ƙaramin ƙaho yana da idanu kamar na mutum, yana kuma da baki, yana hurta maganganu na fariya.”


Ya ce mini, “Zan sanar da kai abubuwan banhaushi, da za su faru nan gaba, gama wahayin ya shafi ƙayyadadden lokaci na ƙarshe.


Na ga ragon ya kai karo wajen yamma da wajen kudu, da wajen arewa. Ba wata dabbar da ta iya karawa da shi, ba wanda kuma zai iya kuɓuta daga ikonsa, ya yi yadda ya ga dama, ya ɗaukaka kansa.


Gama ga shi, zan sa wani makiyayi a ƙasan nan, wanda ba zai kula da masu lalacewa ba, ko waɗanda suka warwatse, ko ya warkar da gurgu, ko ya ciyar da waɗanda suka ragu, amma zai ci naman masu ƙiba, ya farfashe kofatonsu.


“Ba na iya yin kome ni kaɗai. Yadda nake ji, haka nake yin hukunci. Hukuncina kuwa na adalci ne, domin ba nufin kaina nake bi ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni.


Domin na sauko daga Sama, ba domin in bi nufin kaina ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni.


Sun haɗa kai domin su yi dukan abin da ka ƙaddara zai auku, bisa ga ikonka da nufinka.


Gama Ubangiji Allahnku, Allahn alloli ne, da Ubangijin iyayengiji. Shi Allah mai girma ne, mai iko, mai bantsoro, wanda ba ya son zuciya, ba ya karɓar hanci.


Kada ku yarda kowa yă yaudare ku ko ta halin ƙaƙa, domin wannan rana ba za ta zo ba, sai an yi fanɗarewar nan, sarkin tawaye kuma ya bayyana, wato, hallakakken nan.


Shi ne magabci, mai ɗaukaka kansa, yana gāba da duk abin da ya shafi sunan Allah, ko kuma wanda ake yi wa ibada. Har ma yakan zauna a Haikalin Allah, yana cewa, shi ne Allah.


A sa'an nan ne fa sarkin tawayen zai bayyana, Ubangiji Yesu kuwa zai hallaka shi da hucin bakinsa, ya kuma shafe shi da bayyanarsa a ranar komowarsa.


“Allah Maɗaukaki, Allah Ubangiji ya sani, bari Isra'ilawa kuma da kansu su sani. Idan tayarwa ce, ko kuwa mun yi wa Ubangiji rashin aminci ne, to, kada ku bar mu da rai yau.


sai dai a lokacin busa ƙahon da mala'ika na bakwai zai busa ne, za a cika asirtaccen nufin nan na Allah, bisa ga bisharar da ya yi wa bayinsa annabawa.


Amma aka ba matar fikafikan nan biyu na babban juhurman nan, don ta tashi ta guje wa macijin nan, ta shiga jeji, ta je wurin da za a cishe ta a lokaci ɗaya, da lokatai, da rabin lokaci.


Na kuma ga wata dabba tana fitowa daga cikin teku, mai ƙaho goma, da kawuna bakwai, da kambi goma a kan ƙahoninta, da kuma wani suna na saɓo a kawunanta.


domin Allah ya nufe su da zartar da nufinsa, su zama masu ra'ayi ɗaya, su bai wa dabbar nan, mulkinsu, har a cika Maganar Allah.


Sai ya ɗauke ni ya tafi da ni zuwa jeji, Ruhu yana iza ni, sai na ga wata mace a kan wata dabba ja wur, duk jikin dabbar sunayen saɓo ne, tana kuma da kawuna bakwai, da ƙaho goma.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan