Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 11:32 - Littafi Mai Tsarki

32 Waɗanda suka ta da alkawarin kuma, sarki zai ƙara dulmuyar da su ta wurin daɗin bakinsa. Amma waɗanda suka san Allahnsu za su tsaya da ƙarfi su yi wani abu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

32 Ta wurin daɗin baki zai gurɓata waɗannan da suka karya alkawari, amma mutanen da suka san Allahnsu za su yi tsayin daka su yi jayayya da shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 11:32
27 Iomraidhean Croise  

“Kai kuwa ɗana Sulemanu, sai ka san Allah na tsohonka, ka bauta masa da zuciya ɗaya, da kuma yardar rai, gama Ubangiji mai binciken dukan zukata ne, ya kuma san kowane irin nufi da tunani. Idan ka neme shi, za ka same shi, in kuwa ka rabu da shi, shi ma zai yi watsi da kai har abada.


Da na ga mutane sun damu, sai na tashi na yi magana da shugabanni, da sauran jama'a, na ce, “Kada ku ji tsoro, ku tuna da Ubangiji mai iko, mai banrazana, ku yi yaƙi domin 'yan'uwanku, da 'ya'yanku mata da maza, da matanku, da gidajenku.”


Waɗanda suka san ka za su amince da kai, ya Ubangiji, Ba za ka ƙyale duk wanda ya zo gare ka ba.


Idan ka faɗi ƙarya a majalisa, za a hukunta ka, ba za ka kuɓuta ba.


Maƙaryaci yana ƙin wanda ya yi wa ƙarya, mai daɗin baki kuma yakan aikata ɓarna.


Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabcinsa, ko ɗan'uwansa cewa, ‘Ka san Ubangiji’ ba, gama su duka za su san ni, tun daga ƙarami har zuwa babba. Zan gafarta musu laifofinsu, ba kuwa zan ƙara tunawa da zunubansu ba.”


“Wani kuma rainanne zai maye gurbin wancan, shi kuwa ba ɗan jinin sarauta ba ne. Zai taso ba zato ba tsammani, ya ƙwace sarautar ta hanyar zamba.


Sa'ad da suka fāɗi ba za su sami wani taimakon kirki ba, mutane da yawa za su haɗa kai da su, amma da munafunci.


Zan ƙarfafa su, Za su yi tafiya da sunansa, Ni Ubangiji na faɗa.”


Amma ku da kuke yi mini biyayya, ikon cetona zai fito muku kamar rana. Zai kawo warkarwa kamar hasken rana. Za ku fita kuna tsalle kamar 'yan maruƙan da aka fisshe su daga garke.


Rai madawwami kuwa, shi ne su san ka, Allah Makaɗaici na gaskiya, da kuma Yesu Almasihu da ka aiko.


Mun kuma sani Ɗan Allah ya zo, ya yi mana baiwar fahimta domin mu san shi wanda yake na gaskiya. Mu kuwa muna a cikinsa, shi da yake na gaskiya, wato Ɗansa Yesu Almasihu. Shi ne Allah na gasikya da kuma rai madawwami.


Sai aka ba kowannensu farar riga, aka ce musu, su dai huta kaɗan, har a cika adadin abokan bautarsu, wato, 'yan'uwansu, waɗanda za a kashe, kamar yadda su ma aka kashe su.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan