Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 11:21 - Littafi Mai Tsarki

21 “Wani kuma rainanne zai maye gurbin wancan, shi kuwa ba ɗan jinin sarauta ba ne. Zai taso ba zato ba tsammani, ya ƙwace sarautar ta hanyar zamba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 “Magājin wannan sarki zai zama wani mutumin banza wanda ma bai fito daga gidan sarauta ba. Zai taso ba zato ba tsammani, yă ƙwace sarautar ta hanyar zamba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 11:21
17 Iomraidhean Croise  

Akwai mugaye ko'ina, suna ta yanga, Suna ta yabon abin da yake mugunta.


Yakan raina waɗanda Allah ya ƙi su, Amma yana girmama waɗanda suke yi wa Ubangiji biyayya, Kullum yana cika alkawaran da ya yi ko ta halin ƙaƙa,


Kalmominsa sun fi mai taushi, Amma ƙiyayya tana a zuciyarsa, Kalmominsa sun fi mai sulɓi, Amma suna yanka kamar kakkaifan takobi.


Ba wanda zai girmama wawayen mutane, ko kuma ya ce da mazambata suna da aminci.


“Wani sarki zai ɗauki matsayinsa, zai aiki mai karɓar haraji cikin daularsa, amma ba da daɗewa ba za a kashe shi, ba cikin hargitsin yaƙi ba.


Waɗanda suka ta da alkawarin kuma, sarki zai ƙara dulmuyar da su ta wurin daɗin bakinsa. Amma waɗanda suka san Allahnsu za su tsaya da ƙarfi su yi wani abu.


Sa'ad da suka fāɗi ba za su sami wani taimakon kirki ba, mutane da yawa za su haɗa kai da su, amma da munafunci.


Ba za a daɗe ba, wani daga cikin danginta zai tasar wa sojojin sarkin arewa da yaƙi, ya shiga kagararsu, ya ci su da yaƙi.


Wannan shi ne hukuncin da tsarkaka, Masu tsaro suka shawarta, Suka yanke domin masu rai su sani Maɗaukaki yake sarautar 'yan adam, Yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama, Yakan sa talaka ya zama sarki.’


Ina duban ƙahonin, sai ga wani ƙaho, ɗan ƙanƙane, ya ɓullo a tsakiyarsu. Sai aka tumɓuke ƙaho uku na fari daga cikinsu. Wannan ƙaramin ƙaho yana da idanu kamar na mutum, yana kuma da baki, yana hurta maganganu na fariya.”


“A wajen ƙarshen mulkinsu, sa'ad da muguntarsu ta kai intaha, wani mugun sarki mai izgili, mayaudari, zai fito.


Ta wurin mugun wayonsa zai sa cin hanci ya haɓaka. Zai ɗaukaka kansa a ransa. Zai hallaka mutane da yawa, ba zato ba tsammani, har ma zai tasar wa Sarkin sarakuna, amma za a hallaka shi ba ta hannun mutum ba.


Wani ƙaramin ƙaho kuma ya tsiro daga cikin ɗayansu, ya yi girma ya ƙasaita ƙwarai. Ya nuna ikonsa wajen gabas, da wajen kudu, da wajen ƙasa mai albarka.


Ubangiji ya riga ya yi umarni a kanka cewa, “Sunanka ba zai ci gaba ba, Zan farfashe sassaƙaƙƙun siffofi Da siffofi na zubi daga gidan gumakanka. Zan shirya maka kabari, gama kai rainanne ne.”


Na fāɗa masa zan hukunta gidansa har abada saboda 'ya'yansa sun faɗi mugayen maganganu a kaina. Eli kuwa ya sani, amma bai kwaɓe su ba.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan