Daniyel 11:18 - Littafi Mai Tsarki18 Daga nan zai yunƙura zuwa ƙasashen gaɓar teku, ya ci da yawa daga cikinsu, amma wani jarumi zai kawo ƙarshen fāɗin ransa. Zai sa fāɗin ransa ya koma masa. Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 202018 Sa’an nan zai mai da hankalinsa zuwa ƙasashe a bakin kogi, zai kuma kama da yawansu, amma wani komanda zai kawo ƙarshen faɗin ransa, zai kuma sa faɗin ransa yă koma masa. Faic an caibideil |
su kuwa sani ni ne wanda yake hukunta musu. “Amma zan bar waɗansu, in aika da su ga al'ummai da manisantan ƙasashe inda ba a ji labarin sunan da na yi ba, ba a kuwa ga girmana da ikona ba, wato zuwa Tarshish, da Libiya, da Lidiya, duk da gwanayen maharbanta, Rosh da Tubal, da kuma Helas. Za su ba da labarin girmana ga waɗannan al'ummai.