Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 11:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Sarkin arewa kuwa zai tara babbar rundunar soja fiye da ta dā. Bayan waɗansu shekaru kuwa zai kama hanya da babbar rundunar soja, da kayan faɗa masu yawan gaske.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Sarki Arewa kuma zai ƙara tara babbar rundunar soja, wadda ta fi ta dā girma; bayan waɗansu shekaru kuma, zai tafi yaƙi da babbar rundunar mayaƙa cike da kayan yaƙi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 11:13
6 Iomraidhean Croise  

Ganin ya kashe sojoji masu ɗumbun yawa, sai ya yi girmankai, amma nasararsa ba mai ɗorewa ba ce.


“A waɗannan kwanaki mutane da yawa za su tashi gāba da sarkin kudu. Amma waɗansu 'yan kama-karya za su taso daga jama'arka da niyya su cika abin da wahayin ya ce, amma za a fatattaka su.


“A lokaci na ƙarshe sarkin kudu zai tasar masa, sarkin arewa kuwa zai tunzura, ya tasar masa da karusai da mahayan dawakai, da jiragen ruwa da yawa. Zai ratsa ƙasashe, ya ci su da yaƙi, ya wuce.


Sai mutumin da yake sāye da rigar lilin ɗin, wanda yake tsaye a gaɓar kogin ya ɗaga hannuwansa sama, sa'an nan ya rantse da wanda yake rayayye har abada, ya ce, “Za a yi shekara uku da rabi. Za a kammala waɗannan abubuwa, sa'ad da aka gama ragargaje ikon tsarkakan mutane.”


A raba shi da hankali irin na mutane, A ba shi irin na dabba. Zai zauna a wannan hali har shekara bakwai.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan