Daniyel 11:12 - Littafi Mai Tsarki12 Ganin ya kashe sojoji masu ɗumbun yawa, sai ya yi girmankai, amma nasararsa ba mai ɗorewa ba ce. Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 202012 Sa’ad da zai kawar da rundunar, sarkin Kudu zai cika da girman kai zai kuma kashe mutane dubbai, duk da haka ba zai kasance mai nasara ba. Faic an caibideil |
Maimakon haka, sai ka nuna wa Ubangiji girmankai, har ka sa aka kawo maka, kai da fādawanka, da matanka, da ƙwaraƙwaranka, tasoshin Haikalin Ubangiji, kuka sha ruwan inabi a cikinsu. Kuka yabi gumakan zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba su ji, ba su gani, ba su da ganewar kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.