Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 10:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Aka bar ni, ni kaɗai, na ga wannan babban wahayi, ni kuwa ba ni da sauran ƙarfi. Fuskata ta sauya, ta turɓune, ba ni da sauran ƙarfi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Sai aka bar ni ni kaɗai, ina juyayi wannan babban wahayi, ba ni da sauran ƙarfi, fuskata ta yamutse kuma ba ni da sauran ƙarfi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 10:8
15 Iomraidhean Croise  

Rana ta yi sama a sa'ad da Yakubu ya wuce Feniyel domin yana ɗingishi saboda kwatangwalonsa.


Musa kuwa ya ce, “Bari in ratse, in ga wannan abin banmamaki da ya sa kurmin bai ƙone ba.”


Sai wani mai kama da ɗan adam ya taɓa leɓunana, sa'an nan na buɗe baki, na yi magana, na ce wa wanda yake tsaye gabana, “Ya shugabana saboda wannan wahayi ciwo ya kama ni, ba ni da sauran ƙarfi.


Ƙaƙa zan iya magana da kai, ya shugabana? Yanzu ba ni da sauran ƙarfi, ba ni kuma da sauran numfashi.”


“Ni Daniyel na firgita ƙwarai, fuskata ta yi yaushi. Amma na riƙe al'amarin duka a zuciyata.”


Ni Daniyel kuwa na siƙe, na yi ciwo, har na kwanta 'yan kwanaki, sa'an nan na tashi na ci gaba da aikin sarki. Wahayin ya shige mini duhu, ban gane shi ba.


Na ga ya zo kusa da ragon, ya husata da shi ƙwarai, sai ya gabza wa ragon karo. Ya kakkarya ƙahonin nan nasa biyu. Ƙarfin ragon ya kāsa, ba ya iya kare kansa daga bunsurun. Bunsurun ya buge shi ƙasa ya tattake shi. Ba wanda ya iya ceton ragon daga bunsurun.


Sa'ad da na ji, sai jikina ya yi rawa, Leɓunana suka raurawa. Ƙasusuwana suka ruɓe, sai na yi rawar jiki. Zan yi shiru in jira ranar wahala da za ta zo A kan waɗanda suka kawo mana yaƙi.


Da almajiran suka ji haka, sai suka faɗi ƙasa, tsoro ya kama su.


Ya rasa abin da zai faɗa ne, don sun tsorata da gaske.


To, lokaci na zuwa, har ma ya yi, da za a warwatsa ku, kowa yă koma gidansu, ku bar ni ni kaɗai. Duk da haka kuwa ba ni kaɗai nake ba, domin Uba na tare da ni.


Don kada kaina yă kumbura kuma saboda mafifitan wahayan da aka yi mini, sai aka saka mini wata cuta, wadda ta zama mini ƙaya, jakadan Shaiɗan, don yă riƙa wahalshe ni, don kada kaina ya kumbura.


Da na gan shi, sai na fāɗi a gabansa kamar na mutu. Amma ya ɗora mini hannunsa na dama, ya ce, “Kada ka ji tsoro. Ni ne na Farko. Ni ne na Ƙarshe,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan