Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 10:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Jikinsa kamar lu'ulu'u yake, fuskarsa kamar walƙiya, idanunsa kuma kamar harshen wuta, hannunwansa da ƙafafunsa kuwa kamar gogaggiyar tagulla, muryarsa kamar ta babban taron jama'a.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Jikinsa kamar lu’ulu’u yake, fuskarsa kuma kamar walƙiya, idanunsa kamar harshen wuta, hannuwansa da ƙafafunsa kamar gogaggiyar tagulla, muryarsa kuma kamar amon babban taron jama’a.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 10:6
18 Iomraidhean Croise  

A jeri na huɗu, a sa beril, da onis, da yasfa. Za a sa su cikin tsaiko na zinariya.


Hannuwansa kyawawa ne, Saye da ƙawanen da aka yi musu ado da duwatsu masu daraja. Ƙugu nasa sumul sumul ne kamar hauren giwa da aka manne da yakutu.


Talikan kuma suka yi ta giftawa suna kai da kawowa kamar walƙiya.


Ga kamannin ƙafafun da yadda aka yi su. Suna ƙyalƙyali kamar duwatsu masu daraja. Dukansu huɗu fasalinsu ɗaya ne. An yi su kamar wata ƙafa tana cikin wata ƙafa.


Sa'ad da suke tafiya, sai na ji motsin fikafikansu kamar amon ruwa, kamar kuma muryar tsawar Maɗaukaki, kamar hayaniyar runduna. Idan sun tsaya cik, sai su saukar da fikafikansu.


Ƙafafunsu miƙaƙƙu ne, tafin sawayensu yana kama da na maraƙi, suna walƙiya kamar gogaggiyar tagulla.


Da na duba, sai na ga ƙafa guda huɗu kusa da kerubobin. Kowane kerub yana da ƙafa ɗaya kusa da shi. Ƙafafun suna ƙyalli kamar wani dutse mai daraja.


Sa'ad da ya kai ni can sai ga wani mutum, kamanninsa sai ka ce tagulla, yana riƙe da igiyar rama da wani irin ƙara na awo a hannunsa, yana tsaye a bakin ƙofa.


Da na duba, sai ga siffa wadda dake da kamannin mutum. Daga kwankwason siffar zuwa ƙasa yana da kamannin wuta, daga kwankwason kuma zuwa sama yana da haske kamar na tagulla.


Sai kamanninsa suka sāke a gabansu, fuskarsa ta yi annuri kamar hasken rana, tufafinsa kuma suka yi fari fat suna haske.


Kamanninsa suna haske kamar walƙiya, tufafinsa kuma farare fat kamar dusar ƙanƙara.


Yana yin addu'a, sai kama tasa ta sāke, tufafinsa kuma suka yi fari fat, har suna ɗaukar ido.


Sa'an nan na ga wani ƙaƙƙarfan mala'ika yana saukowa daga sama, lulluɓe da gajimare, da bakan gizo a bisa kansa, fuskarsa kamar rana, ƙafafunsa kuma kamar ginshiƙan wuta.


Idanunsa kamar harshen wuta suke, kansa da kambi da yawa, yana kuma da wani suna a rubuce, wanda ba wanda ya sani sai shi.


“Ka kuma rubuta wa mala'ikan ikkilisiyar da take a Tayatira haka, ‘Ga maganar Ɗan Allah, mai idanu kamar harshen wuta, mai ƙafafu kamar gogaggiyar tagulla.


na biyar onis, na shida yaƙutu, na bakwai kirisolat, na takwas beril, na tara tofaz, na goma kirisofaras, na sha ɗaya yakinta, na sha biyu kuma ametis.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan