Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 10:21 - Littafi Mai Tsarki

21 Zan faɗa maka abin da yake rubuce a littafin gaskiya. Ba wanda zai taimake ni yaƙi da waɗannan, sai dai Mika'ilu shugabanka.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 amma da farko zan faɗa maka abin da aka rubuta a cikin Littafin Gaskiya (Babu wanda ya taimake ni yaƙi da waɗannan sai dai Mika’ilu, sarkinku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 10:21
14 Iomraidhean Croise  

Shugaban ƙasar Farisa ya tare ni har kwana ashirin da ɗaya, amma Mika'ilu, ɗaya daga cikin shugabanni, ya zo ya taimake ni, ya tsaya wurin sarakunan Farisa.


“A wannan lokaci Mika'ilu babban shugaba wanda yake lura da jama'arka zai bayyana. A lokacin za a yi tashin hankali irin wanda ba a taɓa yi ba, tun da aka yi duniya. Amma a lokacin za a ceci jama'arka waɗanda aka rubuta sunayensu cikin littafi.


“Amma kai, Daniyel, sai ka rufe maganar, ka kuma kulle littafin, har zuwa ƙarshen lokaci. Mutane da yawa za su yi ta kai da kawowa, ilimi kuma zai ƙaru.”


Wannan wahayi na kwanaki wanda aka nuna maka gaskiya ne, asiri ne kuma, kada ka faɗa, gama zai daɗe kafin a yi.”


Ya zo, ya ce mini, “Ya Daniyel, na zo ne don in ba ka hikima da ganewa.


Sai ka sani, ka kuma gane, daga lokacin da aka umarta a sāke gina Urushalima har zuwa lokacin da shugaba, Masiha, zai zo, za a yi shekara arba'in da tara, da shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu. Za a sāke gina ta a yi mata tituna da kagara.


Hakika Ubangiji ba yakan aikata kome ba, Sai da sanin bayinsa annabawa.


Wannan kuwa daidai yake da maganar annabawa, yadda yake a rubuce cewa,


Haka Ubangiji ya ce, shi da ya bayyana waɗannan abubuwa tun zamanin dā.


Amma lokacin da babban mala'ika, Mika'ilu yake fama da Iblis, suna mūsu a kan gawar Musa, shi Mika'ilu bai yi garajen ɗora masa laifi da baƙar magana ba, sai dai ya ce, “Ubangiji yă tsawata maka.”


Sai yaƙi ya tashi a sama, Mika'ilu da mala'ikunsa suna yaƙi da macijin nan, macijin kuma da mala'ikunsa suka yi ta yaƙi,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan