Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 10:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Ya ce, “Ya kai, mutumin da ake sonka ƙwarai, kada ka ji tsoro, salama a gare ka, ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali!” Sa'ad da ya yi magana da ni, na sami ƙarfi na ce, “Yanzu sai shugabana ya yi magana, ka sa na sami ƙarfi.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Ya kuma ce, “Kada ka ji tsoro, ya kai mutumin da ake fahariya, salama a gare ka! Ka ƙarfafa yanzu; ka yi ƙarfin hali.” Sa’ad da ya yi magana da ni, sai na samu ƙarfi na ce, “Ka yi magana ranka yă daɗe, tun da yake ka sa na sami ƙarfi.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 10:19
29 Iomraidhean Croise  

Ka amsa mini sa'ad da na yi kira gare ka, Da ƙarfinka ka ƙarfafa ni.


Ku faɗa wa dukan wanda ya karai, ku ce, “Ka ƙarfafa, kada kuwa ka ji tsoro! Allah yana zuwa domin ya kuɓutar da kai, Yana zuwa domin ya ɗauki fansa a kan abokan gābanka.”


Kada ka ji tsoro, ina tare da kai, Ni ne Allahnka, kada ka bar kome ya firgita ka. Zan sa ka yi ƙarfi, in kuma taimake ka, Zan kiyaye ka, in cece ka.


Ubangiji ya ce, “Isra'ila, ku kima ne marasa ƙarfi kuma, Kada ku ji tsoro, zan taimake ku. Ni Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ni ne mai fansarku.


Mai kamannin mutum ɗin nan kuma ya sake taɓa ni, ya kuma ƙarfafa ni.


A lokacin da ka fara roƙe-roƙenka sai aka ba da umarni, na kuwa zo domin in faɗa maka, gama ana sonka ƙwarai. Sai ka fahimci maganar da wahayin.


Duk da haka yanzu sai ku yi ƙarfin hali, kai Zarubabel, da kai Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da dukanku mutanen ƙasar, ku kama aikin, gama ina tare da ku. Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.


Ya jama'ar Yahuza da jama'ar Isra'ila, kamar yadda kuka zama abin la'antarwa a cikin al'ummai, haka kuma zan cece ku, ku zama masu albarka, kada ku ji tsoro, amma ku himmantu.


“Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, ku himmantu, ku da kuke jin magana ta bakin annabawa a waɗannan kwanaki tun lokacin da aka ɗora harsashin ginin Haikalin Ubangiji Mai Runduna, don a gina Haikalin.


To, 'yan'uwan nan mata suka aika masa, suka ce, “Ya Ubangiji, ga shi, wanda kake ƙaunan nan ba shi da lafiya.”


Don haka Yahudawa suka ce, “Dubi yadda yake ƙaunarsa!”


Yesu kuwa na ƙaunar Marta da 'yar'uwarta, da kuma Li'azaru.


Na bar ku da salama. Salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada ku damu, kada kuma ku ji tsoro.


Na faɗa muku wannan ne domin a gare ni ku sami salama. A duniya kuna shan wuya, amma dai ku yi farin ciki, ai, na yi nasara da duniya.”


Da Yesu ya ga uwa tasa, da almajirin nan da yake ƙauna suna tsaye kusa, ya ce wa uwa tasa, “Iya, ga ɗanki nan!”


Sai Bitrus ya waiwaya ya ga almajirin nan da Yesu yake ƙauna yana biye da su, wato wanda ya jingina gab da Yesu lokacin cin jibin nan da ya ce, “Ya Ubangiji, wane ne zai bāshe ka?”


Ku zauna a faɗake, ku dāge ga bangaskiyarku, ku yi ƙwazo, ku yi ƙarfi.


amma ya ce mini, “Alherina yā isa, domin ta wajen rashin ƙarfi ake ganin cikar ikona.” Saboda haka sai ma in ƙara yin alfarma da raunanata da farinciki fiye da na da, domin ikon Almasihu ya zauna a tare da ni.


A ƙarshe kuma, ku ƙarfafa ga Ubangiji, ga ƙarfin ikonsa.


Saboda haka, ya kai ɗana, sai ka ƙarfafa da alherin da yake ga Almasihu Yesu.


Ashe, ban umarce ka ba? Ka dāge ka yi ƙarfin hali, kada ka firgita ko ka tsorata, gama Ubangiji Allahnka yana tare da kai duk inda za ka.”


Da na gan shi, sai na fāɗi a gabansa kamar na mutu. Amma ya ɗora mini hannunsa na dama, ya ce, “Kada ka ji tsoro. Ni ne na Farko. Ni ne na Ƙarshe,


Amma Ubangiji ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, ba za ka mutu ba.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan