Sai wani mai kama da ɗan adam ya taɓa leɓunana, sa'an nan na buɗe baki, na yi magana, na ce wa wanda yake tsaye gabana, “Ya shugabana saboda wannan wahayi ciwo ya kama ni, ba ni da sauran ƙarfi.
Dawuda kuwa ya ji tsoro, gama Saul ya fito don ya farauci ransa. Sa'ad da yake cikin jejin Zif, a Horesh, sai Jonatan ɗan Saul, ya zo wurinsa, ya tabbatar masa da kiyayyewar Allah.