Daniyel 10:17 - Littafi Mai Tsarki17 Ƙaƙa zan iya magana da kai, ya shugabana? Yanzu ba ni da sauran ƙarfi, ba ni kuma da sauran numfashi.” Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 202017 Yaya ni bawanka zan iya magana da kai, ranka yă daɗe? Ƙarfina ya ƙare kuma ina numfashi da ƙyar.” Faic an caibideil |
Daniyel kuwa wanda aka laƙaba wa suna Belteshazzar, ya tsaya zugum da ɗan daɗewa, tunaninsa ya ba shi tsoro. Sarki ya ce, “Belteshazzar, kada ka bar mafarkin ko ma'anarsa ya ba ka tsoro.” Sai Belteshazzar ya amsa, ya ce, “Ya shugabana, Allah ya sa mafarkin nan, da ma'anarsa, su zama a kan maƙiyanka.