Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 10:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Shugaban ƙasar Farisa ya tare ni har kwana ashirin da ɗaya, amma Mika'ilu, ɗaya daga cikin shugabanni, ya zo ya taimake ni, ya tsaya wurin sarakunan Farisa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Amma mai mulkin masarautar Farisa ya tsare ni har kwana ashirin da ɗaya. Sai da Mika’ilu, ɗaya daga cikin manya shugabanni, ya zo ya taimake ni, saboda an tsare ni a can tare da sarkin Farisa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 10:13
11 Iomraidhean Croise  

An tsai da aikin Haikalin Allah a Urushalima, sai a shekara ta biyu ta sarautar Dariyus Sarkin Farisa.


“A wannan lokaci Mika'ilu babban shugaba wanda yake lura da jama'arka zai bayyana. A lokacin za a yi tashin hankali irin wanda ba a taɓa yi ba, tun da aka yi duniya. Amma a lokacin za a ceci jama'arka waɗanda aka rubuta sunayensu cikin littafi.


Ai, famarmu ba da 'yan adam muke yi ba, amma da mugayen ruhohi ne na sararin sama, masarauta, masu iko, da waɗanda ragamar mulkin zamanin nan mai duhu take hannunsu.


A gare shi ne aka kammala ku, wanda yake shi ne shugaban dukkan sarauta da iko.


Mun dai yi niyyar zuwa wurinku, ni Bulus, ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, amma Shaidan ya hana.


wanda ya tafi Sama, yake dama ga Allah kuma, mala'iku da manyan mala'iku da masu iko suna binsa.


Amma lokacin da babban mala'ika, Mika'ilu yake fama da Iblis, suna mūsu a kan gawar Musa, shi Mika'ilu bai yi garajen ɗora masa laifi da baƙar magana ba, sai dai ya ce, “Ubangiji yă tsawata maka.”


Sai yaƙi ya tashi a sama, Mika'ilu da mala'ikunsa suna yaƙi da macijin nan, macijin kuma da mala'ikunsa suka yi ta yaƙi,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan