Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 10:12 - Littafi Mai Tsarki

12 Sai ya ce mini, “Kada ka ji tsoro, Daniyel, gama tun daga ran da ka fara sa zuciya ga neman ganewa, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gaban Allahnka, an ji addu'arka, amsar addu'arka ce ta kawo ni.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Sai ya ci gaba da cewa, “Kada ka ji tsoro, Daniyel. Gama tun daga ran da ka fara sa zuciya ga neman ganewa, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gaban Allahnka, an ji addu’arka, amsar addu’arka ce ta kawo ni.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 10:12
26 Iomraidhean Croise  

Na ƙasƙantar da kaina ta wurin yin azumi, Jama'a kuwa suka ci mutuncina.


Ku faɗa wa dukan wanda ya karai, ku ce, “Ka ƙarfafa, kada kuwa ka ji tsoro! Allah yana zuwa domin ya kuɓutar da kai, Yana zuwa domin ya ɗauki fansa a kan abokan gābanka.”


Kada ka ji tsoro, ina tare da kai, Ni ne Allahnka, kada ka bar kome ya firgita ka. Zan sa ka yi ƙarfi, in kuma taimake ka, Zan kiyaye ka, in cece ka.


Ubangiji ya ce, “Isra'ila, ku kima ne marasa ƙarfi kuma, Kada ku ji tsoro, zan taimake ku. Ni Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ni ne mai fansarku.


Sa'an nan za ku yi kira, ni kuwa zan amsa, za ku yi kuka, ni kuwa zan ce muku, ‘Ga ni.’ “Idan kuka kawar da karkiya daga cikinku, kuka daina nuna wa juna yatsa, da faɗar mugayen maganganu,


Zan amsa addu'o'insu tun ma kafin su gama yin addu'a gare ni.


Ya ce mini, “Ya Daniyel, mutumin da ake sonka ƙwarai, ka lura da maganar da zan faɗa maka. Ka miƙe tsaye, gama a wurinka aka aiko ni.” Sa'ad da ya faɗi wannan magana, sai na miƙe tsaye, ina rawar jiki.


Ya ce, “Ya kai, mutumin da ake sonka ƙwarai, kada ka ji tsoro, salama a gare ka, ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali!” Sa'ad da ya yi magana da ni, na sami ƙarfi na ce, “Yanzu sai shugabana ya yi magana, ka sa na sami ƙarfi.”


Waɗannan za su zama farillai a gare su har abada. A rana ta goma ga watan bakwai za su ƙasƙantar da kansu, ba za su yi kowane irin aiki ba, ko ɗan ƙasa, ko baƙon da yake cikinsu.


Wannan rana muhimmiya ce don hutawa a gare su. Za su ƙasƙantar da kansu, wannan farilla ce har abada.


Za a yi tsattsarkan taro a rana ta goma ga watan bakwai domin yin sujada. Ba za a ci abinci ba, ba kuwa za a yi aiki ba.


Sai Yesu ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ku je ku gaya wa 'yan'uwana su tafi ƙasar Galili, a can ne za su gan ni.”


Amma sai mala'ikan ya ce wa matan, “Kada ku ji tsoro, domin na sani Yesu kuke nema, wanda aka gicciye.


Shi kuwa ya ce musu, “Kada ku firgita. Yesu Banazare kuke nema, wanda aka gicciye. Ai, ya tashi, ba ya nan. Kun ga ma wurin da suka sa shi!


Amma mala'ikan ya ce masa, “Kada ka ji tsoro Zakariya, an karɓi addu'arka, matarka Alisabatu za ta haifa maka ɗa, za ka kuma sa masa suna Yahaya.


Mala'ikan kuma ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, Maryamu, kin sami tagomashi a wurin Allah.


Sai mala'ikan ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ga shi, albishir na kawo muku na farin ciki mai yawa, wanda zai zama na dukan mutane.


Sai ya ce musu, “Don me kuka firgita, kuke kuma tantama a zuciyarku?


ya ce, ‘Kada ka ji tsoro Bulus, lalle za ka tsaya a gaban Kaisar, ga shi kuma, Allah ya amsa ya yardar maka duk abokan tafiyarka su tsira.’


Da na gan shi, sai na fāɗi a gabansa kamar na mutu. Amma ya ɗora mini hannunsa na dama, ya ce, “Kada ka ji tsoro. Ni ne na Farko. Ni ne na Ƙarshe,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan