Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 10:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Ya ce mini, “Ya Daniyel, mutumin da ake sonka ƙwarai, ka lura da maganar da zan faɗa maka. Ka miƙe tsaye, gama a wurinka aka aiko ni.” Sa'ad da ya faɗi wannan magana, sai na miƙe tsaye, ina rawar jiki.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Sai ya ce, “Daniyel, kai ne wanda ake ƙauna sosai, ka yi lura da kyau game da kalmomin da zan yi maka magana a kansu, ka tashi yanzu, gama an aiko ni a gare ka.” Sa’ad da ya faɗa mini haka, sai na tashi a tsaye ina rawan jiki.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 10:11
15 Iomraidhean Croise  

“Saboda wannan zuciyata takan kaɗu, Kamar ta yi tsalle daga inda take.


Saboda ke kyakkyawa ce sarki zai so ki, Shi ne maigidanki, sai ki yi masa biyayya.


Ni ta ƙaunataccena ce, yana bukatata.


ko da Nuhu, da Daniyel, da Ayuba suna cikinta, rayukansu ne kaɗai za su ceta saboda adalcinsu, ni Ubangiji na faɗa.


Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, ka tashi tsaye, zan yi magana da kai.”


Ya ce, “Ya kai, mutumin da ake sonka ƙwarai, kada ka ji tsoro, salama a gare ka, ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali!” Sa'ad da ya yi magana da ni, na sami ƙarfi na ce, “Yanzu sai shugabana ya yi magana, ka sa na sami ƙarfi.”


A makon nan uku ban ci wani abincin kirki ba, balle nama ko shan ruwan inabi, ban kuma shafa mai ba.


Sai suka fita, suka ruga a guje daga kabarin, suna rawar jiki a ruɗe. Ba su kuma ce wa kowa kome ba, domin suna tsoro.


Wani daga cikin almajiransa kuwa, wanda Yesu yake ƙauna, yana kishingiɗe gab da Yesu.


Sai Bitrus ya waiwaya ya ga almajirin nan da Yesu yake ƙauna yana biye da su, wato wanda ya jingina gab da Yesu lokacin cin jibin nan da ya ce, “Ya Ubangiji, wane ne zai bāshe ka?”


Amma tashi ka miƙe tsaye, gama na bayyana a gare ka ne da wannan maƙasudi, wato in sa ka mai hidima, mashaidi kuma na abubuwan da ka gani a game da ni, da kuma abubuwa waɗanda zan bayyana maka a nan gaba.


Amma ka tashi ka shiga gari, can za a faɗa maka abin da za ka yi.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan