Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 10:1 - Littafi Mai Tsarki

1 A shekara ta uku ta sarautar Sairus Sarkin Farisa, sai aka aiko da saƙo wurin Daniyel, wanda aka laƙaba wa suna Belteshazzar. Saƙon kuwa gaskiya ne, ya shafi zancen yaƙi, Daniyel kuwa ya fahimci saƙon.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 A shekara ta uku ta Sairus sarkin Farisa, sai aka ba wa Daniyel (wanda ake kira Belteshazar) wahayi. Saƙon kuwa gaskiya ce wadda take tattare da babban yaƙi. Fahimtar saƙon ya zo masa a cikin wahayi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 10:1
28 Iomraidhean Croise  

Maimaitawar mafarkin nan na Fir'auna kuwa, ya nuna cewa Allah ya riga ya ƙaddara al'amarin, hakika kuwa Allah zai tabbatar da shi ba da jimawa ba.


Ubangiji kuwa ya iza Sairus Sarkin Farisa a shekarar da ya ci sarauta, domin a cika maganar da Ubangiji ya faɗa wa Irmiya. Sai ya yi shela a dukan ƙasar mulkinsa, aka kuma rubuta shelar.


Sai suka ba magina da masassaƙa kuɗin, suka kuma ba Sidoniyawa da mutanen Taya abinci, da abin sha, da mai don su kawo itacen al'ul daga Lebanon zuwa teku a Yafa bisa ga izinin da suka samu daga wurin sarki Sairus.


Amma Zarubabel, da Yeshuwa, da shugabannin gidajen kakannin Isra'ila suka ce musu, “Ba abin da za ku yi tare da mu na ginin Haikalin Allahnmu, amma mu kaɗai za mu yi wa Ubangiji Allah na Isra'ila, gini kamar yadda sarki Sairus, wato Sarkin Farisa, ya umarce mu.”


Mutanen kuwa suka yi ijara da mashawarta, da za su sa niyyarsu ta shiririce tun daga zamanin Sairus, Sarkin Farisa, har zuwa zamanin Dariyus, Sarkin Farisa.


Dattawan Yahuza suka yi nasarar ginin ta wurin wa'azin annabi Haggai da Zakariya ɗan Iddo. Suka gama ginin bisa ga umarnin Allah na Isra'ila, da umarnin Sairus, da Dariyus, da Artashate sarakunan Farisa.


“A shekara ta fari ta sarautar sarki Sairus, sai ya ba da izini a sāke gina Haikalin Allah da yake a Urushalima, wurin da za a miƙa sadaka da hadayu na ƙonawa. Sai a aza harsashi da ƙarfi. Tsayinsa zai zama kamu sittin, fāɗinsa kuwa kamu sittin.


Na ce wa Sairus, ‘Kai ne wanda za ka yi mulki domina, Za ka yi abin da nake so ka yi, Za ka ba da umarni, cewa a sāke gina Urushalima, A kuma kafa harsashin ginin Haikali.’ ”


Waɗannan samari huɗu kuwa, Allah ya ba su ilimi, da sanin littattafai, da hikima. Ya kuma yi wa Daniyel baiwar ganewar wahayi da mafarkai.


Daniyel kuwa ya ci gaba har shekarar farko ta sarki Sairas.


Sai sarkin fāda ya laƙaba musu sababbin sunaye. Ya kira Daniyel, Belteshazzar, ya kira Hananiya, Shadrak, ya kira Mishayel, Meshak, sa'an nan ya kira Azariya, Abed-nego.


Na zo ne don in ganar da kai a kan abin da zai faru da mutanenka nan gaba, gama wahayin yana a kan kwanaki na nan gaba ne.”


“Yanzu zan faɗa maka gaskiya. Za a ƙara samun sarakuna uku a Farisa, amma na huɗun zai fi dukansu dukiya. Sa'ad da ya ƙasaita saboda dukiyarsa, zai kuta dukan daularsa ta yi gaba da mulkin Hellas.


“Amma kai, Daniyel, sai ka rufe maganar, ka kuma kulle littafin, har zuwa ƙarshen lokaci. Mutane da yawa za su yi ta kai da kawowa, ilimi kuma zai ƙaru.”


Sai ya ce, “Yi tafiyarka, Daniyel, gama an rufe wannan magana, an kuma kulle ta har ƙarshen lokaci.


Yana da ikon sāke lokatai, Yakan tuɓe sarakuna, ya kuma naɗa waɗansu. Yana ba masu hikima hikima, masu ilimi kuwa fahimi,


Daga baya sai Daniyel wanda aka laƙaba wa suna Belteshazzar, wato irin sunan allahna, yana kuwa da ruhun alloli tsarkaka, ya shigo wurina. Na kuwa faɗa masa mafarkin, na ce,


Yana da ruhun nagari, da ilimi, da ganewa don yin fassarar mafarkai, da bayyana ma'anar ka-cici-ka-cici, da warware al'amura masu wuya. Shi ne wanda sarki ya laƙaba wa suna Belteshazzar. Don haka sai a kirawo maka Daniyel, shi kuwa zai sanar maka da ma'anar.”


Daniyel kuwa ya amsa, ya ce wa sarki, “Riƙe kyautarka, ka ba wani duk da haka zan karanta wa sarki rubutun, in kuma bayyana masa ma'anarsa.


Daniyel kuwa ya bunƙasa a zamanin mulkin Dariyus da na Sairus mutumin Farisa.


Na kuma ji muryar mutum a gāɓar Ulai ta ce, “Jibra'ilu, ka sa wannan mutum ya gane wahayin.”


Wannan wahayi na kwanaki wanda aka nuna maka gaskiya ne, asiri ne kuma, kada ka faɗa, gama zai daɗe kafin a yi.”


To, ga shi, za ka bebance, ba za ka iya magana ba, sai a ran da al'amuran nan suka auku, don ba ka gaskata maganata ba, za a kuwa cika ta a lokacinta.”


Sai mala'ikan ya ce mini, “Rubuta wannan, ‘Albarka tā tabbata ga waɗanda aka gayyata, zuwa cin abincin bikin Ɗan Ragon nan.’ ” Ya kuma ce mini, “Wannan ita ce Maganar Allah ta gaskiya.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan