Ya Ubangiji, ka kasa kunne ga addu'ar bawanka, da addu'o'in bayinka, waɗanda suke jin daɗin girmama sunanka. Ka ba bawanka nasara yau ka sa ya sami tagomashi a gaban mutumin nan.”
Esta kuwa ta gamshi Hegai, ta kuma sami farin jini a wurinsa, sai nan da nan ya ba ta man shafawa, da rabon abincinta, da zaɓaɓɓun kuyangi guda bakwai daga fādar sarki. Ya kuma kai ta da kuyanginta a wuri mafi kyau na gidan matan kulle.
Sa'an nan sarkin fāda ya ce wa Daniyel, “Ina jin tsoro kada shugaban sarki wanda ya umarta a riƙa ba ku wannan abinci da ruwan inabi ya ga jikinku ba su yi kyau kamar na samarin tsaranku ba, ta haka za ku sa in shiga uku a wurin sarki.”
ya kuma tsamo shi daga dukan wahala tasa, ya ba shi farin jini da hikima a gun Fir'auna, Sarkin Masar, shi kuwa ya naɗa shi mai mulkin Masar, ya kuma danƙa masa jama'ar gidansa duka.