Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 1:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Daniyel kuwa ya ƙudura a ransa, ba zai ƙazantar da kansa da cin abinci iri na sarki da shan ruwan inabinsa ba, don haka ya roƙi sarkin fāda, kada ya ba shi wannan abincin da zai ƙazantar da shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Amma Daniyel ya ƙudura a zuciyarsa ba zai ƙazantar da kansa da abinci da ruwan inabin sarki ba, sai ya tambayi sarkin fada don a ba shi izinin kada yă ƙazantar da kansa ta wannan hanya.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 1:8
22 Iomraidhean Croise  

Ubangiji kuma ya yi wa tsohona Dawuda alkawari ya ce, ‘Ɗanka, wanda zai gāje ka, shi zai gina mini Haikali.’ Yanzu kuwa na yi niyyar gina wannan haikali domin sujada ga Ubangiji Allahna.


Sai jama'ar Allah suka taru suka shiga yi wa Ba'al sujada, a Feyor, Suka ci hadayun da aka miƙa wa matattun alloli.


Zan cika muhimmin alkawarina, In yi biyayya da koyarwarka mai adalci.


Ku rabu da ni, ku masu zunubi! Zan yi biyayya da umarnan Allahna.


Ka tsare ni daga son yin mugunta, Ko kuma in haɗa kai da mugaye cikin muguntarsu, Ka sa kada in taɓa yin tarayya da su a bukukuwansu!


Kada ka yi haɗamar kyakkyawan abincin da yake gabanku, zai yiwu wayo yake so ya yi maka.


Sarki kuwa ya sa a riƙa ba su abinci da ruwan inabi irin nasa kowace rana. A kuma koyar da su har shekara uku. Bayan shekara uku za su shiga yi wa sarki hidima.


Da suka bugu da ruwan inabi, sai suka yi yabon gumakansu na zinariya, da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse.


Da ya iso ya kuma ga alherin da Allah ya yi musu, ya yi farin ciki, ya gargaɗe su duka su tsaya ga Ubangiji da dukan zuciyarsu,


sai dai mu rubuta musu wasiƙa, su guji abubuwan ƙazanta na game da gumaka, da fasikanci, da cin abin da aka maƙure, da kuma cin nama tare da jini.


In kuwa ya zamana ba lalle ne yă yi wa 'yar tasa budurwa aure ba, amma ya tsai da shawara bisa ga yadda ya nufa, ya kuma ƙudura sosai a ransa, a kan tsare ta, to, haka daidai ne.


Sai kowa yă bayar yadda ya yi niyya, ba tare da ɓacin rai ko tilastawa ba, domin Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai.


Waɗanda suka ci kitsen hadayunsu, Suka sha ruwan inabin hadayarsu ta sha? Bari su tashi su taimake ku, Bari su zama mafaka!


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan